Majalisar wakilai ta Amince da Bukatar Buhari na Cin bashin N1trn
- Majalisar wakilai ta Najeriya ta amince Buhari ya ci bashin wani kudin domin karasa ayyukan da ya dauko ya sa a gaba
- Wannan na zuwa bayan da majalisar dattawa ta ki amincewa da bukatar a wani lokaci baya saboda wasu dalilai
- Najeriya na ci gaba da fuskantar tsananin bashin ciki da waje, 'yan kasar na ci gaba da nuna damuwa
FCT, Abuja - Majalisar wakilai a Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na cin bashin Naira biliyan 1 don cike wasu gibin kasafin kudin 2022 da ta kare.
Kwamitin majalisa kan wannan fanni kudi ne ya amince da bukatar a ranar Talata 31 ga watan Janairu, inda za a ci kudin daga babban bankin Najeriya (CBN).
Amincewar zai dauki dukkan bashin da babban bankin CBN ke bin Najeriya da ya N23.7trn, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Majalisar dokokin Najeriya a shekarar da ta gabata ta amince da kari kan kasafin kudin 2022 da ya kai N815 domin ba Buhari damar karasa wasu ayyuka ta hanyar rancen cikin gida.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
CBN na bin gwamnatin Najeriya N23.7trn
Idan baku manta ba, shugaba Buhari ya nemi majalisar da ta amince da musayar bashin N23.7trn da CBN ke bin gwamnatin Najeriya, Daily Post tattaro.
Sai dai, majalisar bata amince da bukatar ba tukuna, inda ta bukaci a kawo mata cikakken bayani da zai biyo bayan bukatar.
A halin yanzu, majalisar ta daga ci gaba da sararan bukatar.
A baya rahoto ya bayyana majalisar dattawa ta ki amincewa da bukatar bayan da wasu 'yan Najeriya ska bayyana turjiya game da bukatar da shugaban ya gabatar.
'Yan Najeriya da kungiyiyin farar hula na ci gaba da nuna damuwa game da yawaita cin bashi da gwamnatin Buhari ke yi.
Atiku ne zai iya daidaita bashin da ake bin Najeriya
A wani labarin, wata kungiyar siyasa ta PDP ta ce, dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ne zai iya daidaita bashin da ake bin Najeriya.
A bayyane yake cewa, duk wanda ya gaji Buhari zai kakaba ma kansa bashin N77trn da ake bin gwamnatin kasar nan.
Kungiyar ta kafa hujja ne da irin kwazon Atiku a fannin da ya shafi mulki da kuma kula da arzikin kasa.
Asali: Legit.ng