Karancin Man Fetur na iya Shafar Jigilar Zaben 2023, Inji hukumar Zabe ta INEC

Karancin Man Fetur na iya Shafar Jigilar Zaben 2023, Inji hukumar Zabe ta INEC

  • Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya ce akwai yiwuwar karancin man fetur ya shafi zaben bana
  • Ya ce matukar za a samu tsaiko ta dalilin man fetur, to dole zai kai ga cikas ga zaben da kowane dan Najeriya ya matsu a yi
  • Ana fama da karancin mai a Najeriya, wannan yasa ake ci gaba da dasa ayar tambaya game da zaben 2023

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya ce, tana bukatar ganawa da shugabannin kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL domin gano ko akwai wadataccen mai da zai kai ga yiwuwar zaben 2023.

Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu yayin da yake tattaunawa da kungiyar direbobi ta NURTW a babban birnin tarayya Abuja a yau Talata 31 g watan Janairu.

Kara karanta wannan

Zamu Tabbatar Da Kun Samu Isasshen Mai Lokacin Zabe: NNPC Ya T

Ya shaida cewa, hukumar zabe ta damu matuka gaya ga halin da kasar ke ciki kan batun da ya shafi man fetur, TheCable ta ruwaito.

Akwai matsala a zaben 2023, inji INEC
Karancin Man Fetur na iya Shafar Jigilar Zaben 2023, Inji hukumar Zabe ta INEC | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

INEC ta damu da karancin man fetur

Yakubu ya kuma shaida cewa, INEC ta damuwa da batun karancin man fetur da kuma yadda ya kawo cikas ga harkar sufuri a Najeriya cikin kwanakin nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“Gaskiyar itace tsarinmu zai iya tabuwa saboda karancin wannan kaya.
“Saboda wannan dalilin, hukumar a yammacin yau za ta gana da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) don duba ga yadda za a shawo kan matsalar.”

Ya bayyana cewa, ganawar za ta duba hanyoyin da za su kai ga samar da wadataccen man fetur don tabbatar da tsarin INEC ya tafi daidai, rahoton Peoples Gazette.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Sabon Salo: An Hana Mutane Marasa Katin Zabe Shiga Fadar Babban Sarki A Najeriya

“Ina son tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa za mu ci gaba da tuntubar kowace hukuma ta gwamnati don ganin an yi zaben 2023 cikin lumana.”

Za a samu isasshen man fetur

A nasa bangaren, kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce za a samu wadataccen mai a lokutan babban zaben kasar nan.

Wannan na fitowa bayan da shugaban INEC ya kai ziyara ofishin NNPCL a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban NNPCL, Mele Idris Kyari ya shaidawa INEC cewa:

"Zamu hada kai da direbobinku domin fahimtar wuraren da bamu da gidajen mai saboda mu bukaci wasu yan kasuwa su shigo lamarin don a samawa motocinku 100,000 da kuke fadi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel