Bidiyon Magidanci Na Bayyana Rashin Kaunar da Yake wa Diyarsa mai Shekaru 21 ya Firgita Jama'a

Bidiyon Magidanci Na Bayyana Rashin Kaunar da Yake wa Diyarsa mai Shekaru 21 ya Firgita Jama'a

  • Wani mahaifi ya yadu a soshiyal midiya bayan ya bayyana dalilin da yasa ya dauki karan tsana ya dorawa 'diyarsa mai shekaru 21
  • Kamar yadda mahafin nata cike da alhini ya bayyana, 'diyar tasa ta fari na da son kanta, mummunar dabi'a, kuma ba ta mutunta shi
  • A bidiyon, ya kara da bayyana yadda yake matukar kaunar 'diyarsa mai shekaru 19 kuma yake sonta fiye da ta farkon

Wani mahaifin 'ya'ya biyu ya yi fallasa cike da alhini kan yadda ya tsani 'diyarsa ta fari mai shekaru 21.

Ya yi ikirari a bidiyon cewa 'diyar tasa ta fari ta ke da son kanta, mummunar dabi'a, kullmn tana shiga masa hanci, kuma ba ta mutunta shi.

Magidanci
Bidiyon Magidanci Na Bayyana Rashin Kaunar da Yake wa Diyarsa mai Shekaru 21 ya Firgita Jama'a. Hoto daga @pleasedonttellanyonepod/TikTok
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Matashiya Yar Arewa Da Dirarriyar Sura Ya Girgiza Intanet, Mijinta Ya Mata Yayyafin Kudi

A cewarsa, yana da 'ya'ya biyu mata, amma ya fi son 'yarsa mai shekaru 19 fiye da misali kan 'diyarsa mai shekaru 21.

"Sirrin zuciya na shi ne ba na kaunar 'yata ta fari. Tana shiga hancina, bata da hali mai kyau, tana son kanta da yawa kuma tana musguna min a matsayina na mahaifinta. Ina da 'ya'ya biyu. Duk mata, 'daya 'yar shekara 19 'dayar kuma shekararta 21."

Martanin 'yan soshiyal midiya

@ark210 ya rubata:

"Mummunan halinta ya danganta da ko kai waye."

@ingriiddd ya ce:

"Iyaye da dama su na da na gaban goshi, ina mai tabbatar muku shima 'diyarsa ta farin bata son sa shima abun dariya."

@Renss ya kara da cewa:

"Yanzu bai damu ba idan ta ga wannan?"

@derey ya yi tsokaci:

"Yanzu fa idan ta ga wannan, ina tunanin yadda zan ji idan wannan mahaifina ne 'dan uwa."

Kara karanta wannan

Bidiyo:Matar aure ta Kama Mijinta Dumu-dumu da Budurwarsa a Wurin Cin Abinci, An Tafka Dirama

@nikdnice1 ya yi martani:

"Iyaye da dama ba sa kaunar 'ya'yansu wani lokaci. Ina mamaki idan yana son ta. Zan so ganin martanin ta."

@user470859413349 ya yi martani:

"A matsayinka na mahaifi, za ka iya so ko ka ki so a lokaci daya, ko wasu lokuta."

@Stephanie Katrel ta yi kari:

"Ina da tabbaci 'diyarsa ta sani shiyasa ta ke musguna mishi."

@aymansamucumar ya yi tsokaci:

"Me yasa ku ke tunanin ita ce yar lelensa."

@Julia Salgadi ta ce:

"Wannan ya tashi daga sirri. Ka riga ka fallasa!"

@MC MK ta rubuta:

"Za ka iya kin wani daga cikin iyalanka amma kuma kana kaunarshi."

@bossmanebuchanan ya yi martani:

"Iyaye da dama suna tunanin hakan daidai ne amma bai kamata ka fallasa hakan ba."

'Dan Najeriya ya je biki da akwatin kudi, ya dinga wurga bandira

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya ya halarci shagalin aure da akwati shakare da sabbin kudi.

Ya tsaya gaban amarya da nago inda ya dinga wurga musu bandiran sabbin kudin ba tare da ya warwaresu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel