Cikin Mutum 20, An Zabi 7 Da Cikinsu Wanda Daya Zai Maye Gurbin Akanta Janar

Cikin Mutum 20, An Zabi 7 Da Cikinsu Wanda Daya Zai Maye Gurbin Akanta Janar

  • Komai ya kankama don nada sabon tabataccen Akawun gwamnati watau Akanta Janar AGF
  • Gwamnatin tarayya ta shirya nada sabon AGF sama da watanni shida da dakatar da Ahmed Idris
  • An sallami tsohon Akanta Janar da kuma mukaddashi ne bisa zargin almundahana da rashawa

Abuja - Gwamnatin tarayya ta zabi mutum bakwai cikin Diraktoci guda ashirin da suka nemi kujerar Akanta Janar na tarayya AGF.

Mutum bakwai na suka yi fice cikin wadanda hukumar ICPC ta tantance a 2022.

Punch ta ruwaito cewa a gwajin farko da ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ta gudanar, diraktoci 10 sun fadi warwas.

Sun samu maki kasa 50% kuma aka zabgesu.

Yemi Esan
Cikin Mutum 20, An Zabi 7 Da Cikinsu Wanda Daya Zai Maye Gurbin Akanta Janar Hoto: Presidency
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Laraba, 25 ga Junairu, 2023, sauran mutum 10 suka samu shiga mataki na biyu sun sha gwaji kan iya amfani da ilmin zamani na ICT.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Sight and Sounds' Ta Shirya Taro Kan Manufofin Asiwaju Bola Tinubu

Diraktoci uku sun fadi, bakwai ne suka yi nasara.

A gwajin karshe, diraktocin bakwai sun yi intabiu a ranar Alhamis.

Wani dan kwamitin gwajin, Dr Ernest Umakhikhe, ya bayyana cewa:

"Muna gayyatar yan takaran da aka lissafa nan domin mu'ayana don nada sabon Akanta Janar na tarayya bayan nasarar da suka samu a mataki na farko da na biyu."

An gama gwajin, yanzu za'a sanar da wanda aka zaba

Intabiyun da aka yi ranar Alhamis shine gwaji na karshe da za'ayi kafin sanar da sabon Akanta janar.

Ana sauraron shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya ta sanar da wanda yayi nasara cikin yan kwanakin nan.

Jerin wadanda suka nemi kujerar

A baya mun kawo muku rahoton yadda hukumar yaki da rashawa ICPC ta tantance mutum 20 da suka nemi maye gurbin kujerar Akanta Janar na tarayya.

Diraktoci daga ma'aikatun gwamnati daban-daban suka nemi kujerar biyo bayan sallamar tsohon AGF, Ahmed Idris, a Yuli 2022 da Ministar kudi tayi bayan hukumar EFCC ta zargesa da almundahanar N109bn.

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

Diraktocin da suka nemi kujerar sun hada da Danladi Comfort, Gombe; Mohammed Yar’Abba, Sokoto; Mufutau Bukola, Oyo; Mahmud Kambari, Borno; Mohammed Dojo, Gombe; da Waziri Samuel, Borno.

Sauran sune Maiden Sakirat, Ogun; Adaramoye Oluwole, Ekiti; Isa Abubakar, Yobe; Ogunsemowo Olakunle, Ogun; Egbokhale Charity, Edo; Ibrahim Jibo, Kano; Ogbodo Nnam, Enugu; da Bakare Juliannah, Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel