Gwamnan CBN Shigo-Shigo Ba Zurfi Ya Yiwa Buhari Kan Lamarin Sauya Fasalin Naira: Ado Doguwa

Gwamnan CBN Shigo-Shigo Ba Zurfi Ya Yiwa Buhari Kan Lamarin Sauya Fasalin Naira: Ado Doguwa

  • Ana cigaba da kai ruwa rana kan lamarin sauya fasalin takardun Naira da wa'adin daina da amfani da tsaffin kudi
  • Alhassan Ado Doguwa ya bayyana abinda da ya fahimta game da wannan sauya fasali na Naira
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kara wa'adin daina amfani da kudin da kwanaki 10

Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana ra'ayinsa game da lamarin saura fasalin Naira da ake kai ruwa rana kansa.

Ado Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Tudun Wada da Doguwa ya ce Gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, kawai rufa-rufa ya yiwa Shugaba Buhari.

Ya ce alamu sun nuna shugaban kasan bai fahimci lamarin ba kawai shigo-shigo ba zarfi aka yi masa.

Doguwa ya bayyana hakan ne a ranar Litnin a shirin Politics Today na ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta yi Alla-Wadai Da Rajamun Da Aka Yiwa Shugaba Buhari a Kano

Yace wannan lamarin sauya fasalin naira zai tayar da tarzoma da ka iya hana iya gudanar da zaben shugaban kasa a 2023.

Doguwa
Gwamnan CBN Shigo-Shigo Ba Zurfi Ya Yiwa Buhari Kan Lamarin Sauya Fasalin Naira: Ado Doguwa Hoto: Doguwa
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaudarar Buhari aka yi

Doguwa ya ce Emefiele bai yiwa Buhari bayanin da ya kamata ba kafin ya amince da lamarin sauya fasalin kudin.

Yace:

"La'alla an bijirowa shugaban kasa da bayanin da bai fahimci tasirinsa ba, saboda haka dole ya yanke gurguwar shawara. Abinda nike shawara hake kuma abinda na fahimta da lamarin kenan."

Doguwa ya ce ya gana da shugaba Buhari ranar Lahadi kuma nuna masa bacin ransa kan Gwamnan CBN, Godwin Emefiele wanda ya ki amsa gayyatar da majalisar tayi masa.

Ado Doguwa yace wata hujjar dake nuna cewa shugaba Buhari bai fahimci lamarin ba tun farko shine dage wa'adin daina amfani da tsaffin kudin da yayi da kwanaki 10.

Kara karanta wannan

Duk Da Rashin Amincewar Ganduje, Buhari Zai Kai Ziyara Jihar Kano a Gobe Litinin

Bankin CBN ya kara wa’adin kashe tsofaffin N200, N500 da N1000

Bankin CBN ya kara wa’adin kashe tsofaffin N200, N500 da N1000.

Gwamnan Babban bankin Najeriya na CBN ya sanar da tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin kudi a Daura.

Wannan ya biyo bayan kukan da manyan masu fada a aji a Najeriya da al'umma suka yi kan wannan lamari.

Mutane sun yiwa shugaban kasa jifa da dutse tare d aihun bamaso yayinda ya ziyarci Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel