Kwalejin Imo Ya Fusata Yayin da Daliba Ta Yi Ikirarin Kammala Karatunta Ta Taimakon Al’aurarta
- Kwalejin fasaha ta Nekede a jihar Imo ya yi Allah-wadai da wani bidiyon da dalibar makarantar ta yada mai daukar hankali
- Wata sanarwa da kwalejin ta fitar ta ce, an fara bincike don gano dalibar da tace al’aurarta ce ta taimake ta ta kamala karatu
- Kwamitin jami’ar ya ce zai bincike tare da sanar da al’umma matakin da ya dayka game da dalibar da ta yi ikrarin
Jihar Imo – Wata dalibar kwalejin fasaha ta tarayya da ke Nekede a jihar Imo ta shiga cakwalkwalin rikici bayan da ta yi ikrarin ba da kanta kafin ta kammala karatunta.
Dalibar da ba bayyana sunanta ba ta yada wani bidiyo a TikTok, inda yace al’aurarta ce ta taimake ta wajen kammala karatun.
Ta bayyana godiya ga Allah da ta samu damar kammala karatun, tare da yiwa makarantar bankwana a ranar karshe.
A bidiyon da ta yada, ta bayyana cewa:
“Omo, yau ce ranar karshe. Sai wata rana Nekede, wannan wahalar ta kare yau. Daga karshe, ni dai na kammala karatu a kwalejin fasaha ta Nekede. Iko ne na Allah da kuma al’aurata.”
Hukumar kwaleji za ta dauki mataki
Da take martani ga batun dalibar, hukumar kwalejin ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin 30 ga watan Janairu ta hannun magatarkadarta, Eucharia Anuna, ta yi Allah wadai da batun
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da farko dai makarantar ta nesanta kanta da wannan batu na dalibar, kuma ta ce ba dabi’a da halin jami’ar da malamanta bane, TheCable ta ruwaito.
Makarantar ra ce wannan batu ne na banza, kuma tabbas za ta dakulo dalibar tare da daukar matakin da ya dace a kanta.
Daga karshe, ta ce za ta yi bincike don gano dalibar kuma za a sanar da mutane dukkan halin da ake ciki a nan gaba.
Dalibi ya sheke yana tsaka da budurwarsa a otal
A wani labarin kuma, kunji yadda gwani dalibin kwalejin fasaha ya sheka kiyama yayin da yake tsaka da cancarewa a otal.
Rahoton da muka samo ya ce, dalibin yana cikin yin jima'i da budurwarsa ne aka turo masa mala'ikan mutuwa.
A cewar majiya, saurayi da bururwar suna tsaka da jima'i ne kawai ya mutu, ya bar budurwar rai a hannun Allah.
Asali: Legit.ng