'Yan Najeriya Sun Yi Farin Ciki da CBN Ya Kara Wa'adin Tsohon Kuɗi
- Yan Najeriya mazauna babban birnin tarayya Abuja sun bayyana farin cikinsu da karin wa'adin musanya kuɗi
- A ranar Lahadi gwamnan babban bankin Najeriya ya bayyana cewa shugaba Buhari ya amince da ƙara kwana 10
- Mutane da dama sun yaba wa matakin karin inda suka bayyana wahalhalun da suka sha sanadin sabon tsarin
Abuja - Wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja sun nuna farin ciki da jin dadi bayan kara wa'adin musanya tsohon kuɗi da sabon da aka canja.
Jaridar Punch ta rahoto cewa a ranar Lahadi, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya sanar da cewa ya samu amincewar shugaban kasa na ƙara kwana 10.
A cewar gwamnan CBN, wa'adin daina amsar tsoffin kuɗin ya matsa daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, 2023 domin samun damar karban tsohon kuɗi daga hannun 'yan Najeriya.
Yadda mutane suka ji bayan kara wa'adin
Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu mazaunan Abuja sun koma majalisa suna tattaunawa kan lamarin bayan jin labarin ƙara wa'adin da kwana 10.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wata mata mai suna Josephine, tace mahaifiyarta ta kira ta a wayar tarho daga kauye domin ta faɗa mata cewa ba ta samu damar musanya tsoffin kuɗinta ba.
Josephine ta bayyana cewa ta shiga damuwa sakamakon mahaifiyarta ba zata samu damar musanya kuɗin ba kafin wa'adin da CBN ya cika.
Ta ce:
"Mun samu labari bayan dawowa daga Majami'a kuma abu na farko da na yi shi ne kiran waya domin sanar da Mamata."
"Na shiga damuwa kan rashin lafiyarta domin sabon tsarin ya rikitata. Lokacin da na faɗa mata an ƙara lokaci ta yi mamaki."
Obinna Ugwu, wani mazaunin Abuja ya bayyana cewa matakin ƙara wa'adin abun a yaba ne.
Ogwu yace duk da ya gama musanya kuɗinsa zuwa sababbi amma ya taya abokansa da makota farin ciki, wadanda har yanzu suke tattare da tsoffin kuɗi.
A kalamansa ya ce:
"Wannan labari ne mai daɗi ga abokaina da har yanzu suke da tsohon kuɗi, ƙarin bai da yawa amma ya fi na 31 ga watan Janairu. Ina mamakin ta ya mutane musamman a kauyuka zasu iya cimma wa'adin farko."
Wani direban Taxi, Miata David Oche, yace ƙara lokacin abu ne mai kyau domin yana hanyar zuwa gidan mai ya siya Fetur da tsohon kuɗin, kawai ya samu labari.
Direban yace:
"Jira sai lokaci ya kure abu ne da ya zama ruwan dare tsakanin 'yan Najeriya kuma ɗabi'a ce da ya kamata mu sauyata. Zaka sha mamaki duk da ƙarin nan wasu zasu jira ranar karshe kafin su kai tsohon kuɗi a basu sabo."
CBN Ya Sha Alwashin Sanya Ido Kan Manyan Dakunan Ajiya Na Bankuna
Saura Kwana 2 Wa'adi Ya Cika, CBN Ya Ɓullo da Shirin Yadda 'Yan Arewa Zasu Samu Sabbin Kuɗi Cikin Sauki
A wani labarin kuma Bayan Kara Wa'adi, CBN Ya Gano Abinda Ke Wahal da Mutane Game da Sabbin Kudi
Babban Bankin Najeriya (CBN) yace zai sa ido sosai kan manyan ɗakunan ajiye kuɗi na Bankunan 'yan kasuwa nufin gano bankunan da ke ɓoye sabbin takardun kuɗi.
Asali: Legit.ng