Ku Samo Mana Babura 2 da Kayan Abinci, ’Yan Bindiga Ga Mazauna Kaye a Jihar Kaduna
- 'Yan bindiga sun nemi a basu kayan abinci a madadin kudin fansa da suka nema daga dangin wadanda suka sace
- Sun ce a basu babura da kayan abinci da barasa kafin su sako mutanen tunda sabbin kudi sun gagara samuwa
- Ana kyautata zaton sauya kudin Najeriya zai kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake ciki a kasar nan
Jihar Kaduna - Wadanda suka yi garkuwa da wasu mutum 14 a kauyen Janjala a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna sun nemi a basu babura sabbi guda biyu, kayan abinci, kwaya da barasa kafin su sako mutanen da suka sace.
City & Crime ta ruwaito cewa, ‘yan bindiga a makon jiya sun sako mutum daga 11 da suka sace a kauyen makwabta da ke kusa da Kadara bayan karbar kayan abinci, kwaya da barasa a matsayin fansa.
Bidiyon Yadda Aka Yi Bushasha Da Bandir-Bandir Din Sabbin Kudi a Wajen Wani Buki Yayin da Ake Nemansu Ido Rufe
Wannan karbar kayan abinci na zuwa ne bayan da suka ki karbar tsoffin kudade N5.3m da aka basu domin sakin mutanen, rahoton Daily Trust.
A bamu babura da abinci - bukatar 'yan bindiga
‘Yan bindigan sun ki sakin sauran mutum tara tare da cewa, dole sai an tara musu kudin fansan da ya kai N30m na sabbin kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana ta wayar salula, sakataren sarkin Janjala, Babangida Usman ya ce, shugaban ‘yan bindigan ya ce, tunda an gaza sama musu sabbin kudi, to a siya musu sabbin babura da kayan abinci.
A cewarsa:
“Don haka, wannan shine yanayin da ahalin wadanda aka sace suke ciki. Kuma ta yaya za a samu kudin siyan babur da kayan abincin ma wata matsalar ce.”
Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba, Muhammad Jalige.
Ba Zamu Karba Kudin da Zasu Zama Takardun Tsire ba: 'Yan Bindiga Sun ki Karbar Tsofaffin N5.3m na Fansa a Kaduna
'Yan kasuwa a Kebbi sun koka kan karancin sabbin Naira
A wani labarin, kunji yadda 'yan kasuwa a jihar Kebbi suka bayyana kokensu kan yadda sabbin kudade ke ka kin samuwa a jihar.
A cewarsu, za su rufe kasuwancinsu saboda babu yadda za su yi su samu abin da suke bukata daga kwastomominsu.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da aka gaza samun sabbin kudi a bankuna gashi kuma ana kokarin daina amfani da tsoffin kudaden da ake dasu a hannu.
Asali: Legit.ng