Ban Zan Taba Kashe Aurena Saboda Maganar Mutane Ba, Inji Matar Da Ta Auri Saurayin Diyarta

Ban Zan Taba Kashe Aurena Saboda Maganar Mutane Ba, Inji Matar Da Ta Auri Saurayin Diyarta

  • Malama Khadija wacce ta auri saurayin 'yarta a jihar Kano ta ce sam ba za ta kashe aurenta ba saboda maganar mutane
  • Matar da ta yi wuff da saurayin diyarta ta ce tunda dai ba Allah madaukakin sarki ta sabawa ba mutane su je chan su karata da maganganunsu
  • Ta ce babu wanda ya tilasta mata yin auren ita da kanta ta yi ra'ayi kuma tana jin dadin zama da angonta

Kano - Malama Khadija, yar Kanon nan da ta auri saurayin diyarta ta sha alwashin cewa ba za ta janye daga kudirinta ba saboda cece-kucen da mutane ke yi a kanta ba.

Matar ta bayyana cewa tunda dai bata sabawa Allah madaukakin sarki ba toh bata damu da abun da mutane ke cewa game da wannan abu da ta aikata ba, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bidiyo:Matar aure ta Kama Mijinta Dumu-dumu da Budurwarsa a Wurin Cin Abinci, An Tafka Dirama

Jihar Kano
Ban Zan Taba Kashe Aurena Saboda Maganar Mutane Ba, Inji Matar Da Ta Auri Saurayin Diyarta Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

An tattaro cewa labarin matakin da Khadija ta dauka na ci gaba da haifar da takkadama a Kano, yayin da mutane da dama ke al'ajabin ko da gaske ne, inda wasu kuma ke muhawara kan halaccin auren a cikin addinin Musulunci.

Ku tuna cewa Khadija ta ba da dalilin kashe tsoron aurenta don auren saurayin diyarta kan cewa bai kamata ita da diyarta su rasa kyakkyawan saurayi kamarsa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ina zaune lafiya da mijina, Khadija

Da take magana a kan takaddamar da hakan ya haifar a cikin ahlinta da jihar, Khadija ta ce bata yi danasani ba.

Khadija ta ce:

"Ina mamakin dalilin da yasa mutane suka sawa aurena ido. Ni da kaina na yanke shawarar. Babu wanda ya yi mun dole. Diyata ta ki amincewa da mutumin, kuma sai na ji cewa bai kamata mu rasa shi ba. Muna cikin kwanciyar hankali a gidan aurenmu kuma ina jin dadin zamana da shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Shekaru 57 da ke Nuna Yarinta, Ta Saka Jar Riga ta Amaren Zamani

"Ina son mutane su sani cewa na tambayi malamai game da halascin wannan auren kuma sun ce babu matsala da wannan. Don haka, ba zan janye daga wannan auren ba. Zama daram dan, bana bukatar shawarar kowa."

Kan zargin da ake yiwa kwamandan Hisban karamar hukumar Rano, Khadija ta ce bai tilasta mata aure ba.

Sai dai kuma, kwamandan Hisbah na jihar ya kafa wani kwamiti don binciken lamarin, rahoton Aminiya.

Daga karanta wasika, Amarya ta fasa aure a ranar jajiberin bikinta

A wani labari na daban, wata amarya ta ce ta fasa bata yin auren ana gobe bikinta bayan ta karanta wata wasika da aka kawowa mai shirin zama mijinta.

Ta dai gano cewa akwai bashi dankare a kansa amma ya boye ya ki gaya mata har ana shirin kwace kadarorinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng