Kwamitin Majalisa Ya Ki Amincewa da Tsawaita Wa’adin Kashe Tsoffin Kudi, Zai Kama Emefiele
- Majalisar wakilai a Najeriya ta ce bata amince da yadda gwamnan CBN ya kara wa'adin kashe tsoffin kudi ba
- Gwamnan ya bayyana cewa, za aci gaba da amfani da tsoffin kudade daga yanzu zuwa 10 ga watan Fabrairu
- Majalisa ta yi barazanar kame gwamnan n CBN matukar bai gama da ita ba a ranr Litinin 30 ga watan Janairu
Kwamitin majalisar wakilai kan abin da ya shafi kudi ya yi watsi da batun kara wa’adin da CBN ya yi na amfani da tsoffin kudi a Najeriya.
Rahoton jaridar Punch ya ce, majalisar ta siffanta karin da wani yunkuri na siyasa domin yaudarar ‘yan Najeriya tare da kuntata tattalin arzikin talakawa.
A tun farko, CBN ya sanya ranar 31 ga watan Janairun 2023 domin daina amfani da tsoffin N200, 500 da N1000 tare da yin wasu sabbi.
Sai dai, a ranar Lahadi 29 ga watan Janairu, bankin ya sanar da kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun bana.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya sanar da karin bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun da ya shafi sabbin kudaden.
Majalisa ta ce ba za ta amince ba
Sai dai, da yake martani ga batunm shugaban masu rinjaye na majalisa, Alhassan Ado Doguwa ya ce majalisa bata amince da wannan karin ba.
Hakazalika, ya ce dole ne majalisar ta bi tanadin kudin dokar CBN sashe na 20 sakin layi na 3,4 da 5.
Hakazalika, ya ce majalisar za ta ba da umarnin a kama gwamnan na CBN tare da kawo shi gaban kwamitin da aka yi kan batun kudi, Channels Tv ta ruwaito.
Ha kuma bayyana cewa, kwamitin zai yi aiki don ganin an biya bukatun ‘yan Najeriya daidai da tanadin da dokar kasa ta tanada.
A cewar Doguwa, dole ne gwamnan CBN ya bayyana a gaban majalisa ko kuma ya fuskanci kamu a ranar Litinin 30 ga watan Janairu.
A fahimtar Doguwa, sabbin ka’idojin CBN na son kawo tsaiko ne kawai gaz aben 2023 da ke gaba a watan gobe.
'Yan Najeriya dai na ci gaba da nuna damuwa game da karancin sabbin kudi, a wasu jihohin har siyar da kudaden ake.
Asali: Legit.ng