'Yan Sanda Sun Zargi ’Yan Ta’addan Ipob da Kashe Wata Jami’arsu a Jihar Imo
- ‘Yan sandan jihar Imo sun zaegi ‘yan ta’addan IPOB da kasha wata jami’arsu a wata musayar wuta da suka yi a jihar
- Rahoto daga bakin wani ganau ya bayyana dalla-dalla yadda ‘yan ta’addan suka hallaka matar a bakin aiki
- Ana yawan samun lokuta da yawa da ‘yan ta’addan IPOB ke yiwa jami’an ‘yan sanda kisan gilla ko kone kayan gwamnati
Jihar Imo - Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta zargin tawagar ta’addancin ta ESN da kashe wata jami’arsu mai suna Chinyere Obialor.
Kungiyar ta’addanci ta ESN wata kungiya ce da ke aiki kafada da kafada da haramtacciyar kungiyar ‘yan aware ta IPOB, ta su Nnamdi Kanu.
Da yake zantawa da jaridar TheCable, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abbatam ya ce, an kashe Obialor ne a wata musayar wuta da aka yi da kungiyar ta ESN.
Ya shaidawa jaridar cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun yi rashin daya daga cikin jami’anmu, mace, a wata kazamar fada da ‘yan IPOB da kuma sashen tsaronta da aka fi sani da ESN.
“A lokacin musayar wuta, sun abin hawansu daya sun tsere. Muna ci gaba da bincike don kamo masu hannu a lamarin.”
Yadda lamarin ya faru daga bakin ganau
Wani ganau ya bayyana cewa, an kashe Obialor ne a wata musayar wuta da ‘yan sandan suka yi da ‘yan ta’addan a yankin Ihitte, kan titin Owerri zuwa Aba na jihar, Sahara Reporters ta tattaro.
A cewar ganau din:
“An kashe ta ne a wata musarar wuta lokacin da ‘yan ta’addan suka yi kwantin bauta a kansu a magamar Ihitte a kan titin Owerri zuwa Aba. ‘Yar asalin yankin Mgbidi a karamar hukumar Oru ta yamma a jihar Imo.
“Tana aiki ne a rundunar sintirin manyan hanyoyi. Tsagerun sun gudu sun bar abin hawansu.”
An kashe jigon APC a Imo
A wani labarin kuma, kun ji yadda wasu ‘yan ta’adda suka kutsa har cikin gida suka hallaka wani jigon APC a jihar Imo.
Wannan lamarin ya faru ne a cikin makon nan, kamar yadda wasu majiyoyi suka tattaro daga shaidun gani da ido.
An kuma ruwaito cewa, wani mutum yam utu yayin da yake shirin gudu bayan jin karar harbin bindiga lokacin harin tsagerun.
Asali: Legit.ng