Ba Ruwan NAF, Jirgi Mara Matuka Ne Ya Saki Bam a Nasarawa, Sule
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya musanta jita-jitar cewa jirgin NAF ne ya kai harin Bam kan makiyaya
- Akalla Makiyaya 27 aka tabbatar sun mutu a wani tashin Bam da ya auku a garin Kwateri mai iyaka tsakanin Nasarawa da Benuwai
- Sule ya bayyana cewa wani jirgi mara matuki ne ya saki bama-baman kuma har yanzun ba'a gano wanda ya turo shi ba
Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, yace harin Bam ɗin da ya faru a Kwateri, kauyen dake tsakanin Nasarawa da Benuwai, ba jirgin soji bane ya aikata.
Gwamna Sule, wanda ya yi jawabi a gidan Talabijin ɗin Arise TV ranar Laraba, ya ce wani Jirgi mara matuki da ba'a san mai sarrafa shi ba ne ya aikata ɗanyen aikin.
A ranar Talatan da ta gabata, akalla mutane 27 ne suka rasa rayukansu biyo bayan harin jirgin saman da ya faɗa kan Makiyaya, wadanda ke jiran Motar da zata ɗauki dabbobinsu.
Ƙungiyar Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN) ta ce harin Bam din ya auku ne bayan Makiyayan sun je karɓo shanu 1,250 da Dakarun gwamnatin Benuwai ta tsare masu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Su wa suka kai harin?
Da yake jawabi sosai kan harin, gwamna Sule ya yi fatali da "Jita-Jitar" da ake yaɗawa cewa Sojin Sama ne ke da alhakin kai harin, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Yace a binciken da aka yi an gano cewa, "Babu jirgin NAF ɗin da ya wuce ta wurin," inda ya ƙara da cewa Jirgi mara matuki ne ya tashi bam kan mutanen kuma har yanzun ba'a gano wanda ya sarrafa jirgin ba.
Sule ya ce:
"Ba abu ne mai sauki ba a kama wani a yanzu saboda baki ɗaya wurin yana cikin wani irin yanayi. Ana ta yaɗa cewa Jirgin Sojin sama ne ya aikata amma a yanzu mun fahimci babu jirgin NAF ɗin da ya bi ta wurin."
"Jirgi mara matuki ne ya gitta ta wurin kuma ya saki bam. Na yi magana da dukkan hukumomin tsaro amma sun ce basu san komai kan lamarin ba. Babu wanda ya ɗauki nauyin harin bam ɗin."
Gwamna Sule ya kara da cewa har yanzu ana kan bincike domin gano ainihin gaskiyar game da harin.
Asiri ya fara tonuwa kan harin tashar jirgin kasan Edo
A wani labarin kuma An Kama Daya Daga Cikin Miyagun Da Suka Yi Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa A Najeriya
Gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa gamayyar jami'an tsaro sun kama mutum daya da ake zargi da hannu a garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a jihar.
A cewar gwwamnan, wanda ake zargin yabfara bayani kuma yana taimaka wa jami'ai domin ceto mutanen da yan ta'addan suka yi awon gaba da su.
Asali: Legit.ng