Za Ku Dandana Kudarku: Malamin Addini Ya Hango Abin da Zai Faru da 'Yan Najeriya

Za Ku Dandana Kudarku: Malamin Addini Ya Hango Abin da Zai Faru da 'Yan Najeriya

  • Fittacen faton Najeriya, Primate Ayodele ya yi wa gwamnan CBN, Godwin Emefiele wankin babban bargo kan wa’adin daina karbar tsoffin kudi
  • Malamin addinin ya ce yan Najeriya za su ci gaba da shan wahala saboda an sauya kudin a lokacin da bai dace ba
  • Ayodele ya ce wannan muguwar shawara ta Emefiele talaka zai shafa ba yan siyasa ba don dai su basa taba rasa mafita

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa yan Najeriya za su shafe tsawon lokaci suna shan wahala saboda manufofin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, wadanda basu dace ba.

Yayin da yake martani ga wa'adin 31 ga watan Janairu da babban bankin kasar ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kudi, Ayodele ya ce Emefiele ya lalata tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Baku isa ba ku karya kasa: Majalisa ta dura kan CBN game da sabbin Naira, ta fadi matakin da za ta dauka

Ya jaddada jawabinsa na cewa sauya fasalin kudi ba zai amfani kasar da komai ba, jaridar PM News ta rahoto.

Emefiele da Ayodele
Za Ku Dandana Kudarku: Malamin Addini Ya Hango Abin da Zai Faru da 'Yan Najeriya, Ya Fadi Mafita Hoto: CBN
Asali: Twitter

Za a ci gaba da fuskantar tabarbarewar tattalin arziki har a gwamnati mai zuwa, Ayodele

Ya yi bayanin cewa sauya fasalin kudi da wa'adin daina kashe su na wahalar da talaka kuma wannan wahalar za ta ci gaba har zuwa gwamnati ta gaba saboda tabarbarewar tattalin arzikin zai ci gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ayodele ya ce:

"Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya lalata tattalin arzikin kasar kuma daga talaka har mai kudi ba za su ji dadin gwamnatin nan ba har zuwa karshenta. Na fadi a baya cewa sauya fasalin kudi ba zai yi wani amfani ba.
"Manufar sauya kudin na shafar talakawa, ba su san shi ba tukuna kuma yana lalata tattalin arzikin da zai kai ga sabuwar gwamnati. Yanzu Najeriya ta fara shan wahala, wannan wahalar zai dade. Kudin zai haifar da shan wahala saboda jama'a za su sha wahala a wannan tsarin sauya kudin."

Kara karanta wannan

Har Sambisa akwai sabbin kudi, mun tura ma'aikata wajen: Gwamnan CBN

Talaka ne zai wahala ba yan siyasa ba

Malamin addinin ya bayyana tsarin sauya kudin a matsayin muguwar shawara a lokacin da bai dace ba saboda ba zai magance rashawa ba domin yan Najeriya za su nemi mafita; maimakon haka talakawa ne za su wahala da wannan aiki na Godwin Emefiele, rahoton Daily Post.

Ya ci gaba da cewa:

"Wannan ba zai shafi yan siyasa ba kai tsaye sai dai talakawa;muguwar shawara ce a lokacin da bai dace ba, sauya kudi ba zai magance rashawa ta koina ba saboda yan siyasa za su samu mafita a koyaushe. Wannan yaki ne da talaka, sune abun yake shafa.
"Emefiele ya sake jefa Najeriya cikin wata matsalar saboda ba zai iya magance wannan abun ba, zai rasa mafita kuma kudaden za su haifar da matsaloli ga tattalin arziki da wahala. Abun zai shafi bankuna suma saboda za mu samu tabarbarewar tattalin arziki. Imma suna yakar yan siyasa ne ko akasin haka, talaka ne zai sha wahala a karshe."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kuyi Hakuri Amma Ba Zamu Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Ba, Emefiele

Uwa ta fasa asusun ajiyar 'ya'yanta don sauya tsoffin kudi da sababbi

A wani labarin, wata uwa ta fasa asusun ajiyar yaranta don kwashe kudaden da suka shafe tsawon shekaru 10 suna tarawa.

Hakan ya kasance ne domin su samu damar sauya tsoffin kudaden da ke ciki da sababbi kafin cikar wa'adin da babban bankin kasa, CBN ya diba na daina amfani da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel