Ko Sambisa Mun Tura Ma'aikata Su Canzawa Mutane Tsaffin Kudi, Emefiele

Ko Sambisa Mun Tura Ma'aikata Su Canzawa Mutane Tsaffin Kudi, Emefiele

  • Gwamnan CBN ya lissafo garuruwan da ake tunanin babu sabbin kudi amma sun tura jami'an bankin
  • Mafi akasarin garuruwan na cikin inda Boko Haram suka kwace a baya kuma kan iyakan Najeriya da kasar Kamaru da Chadi
  • Emefiele ya ce masu kukan basu ganin sabbin kudi fa sun san abinda suke yi, kuma ba za'a biye musu ba

Abuja - Gwamnan bankin tarayyar Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana dalilin da yasa ba zasu dage wa'adin ranar daina amfani da tsaffin kudaden Naira ba.

Emefiele ya bayyana hakan ranar Talata yayin hira da manema labarai biyo bayan zaman kwamitin kudi MPC a birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya jaddada cewa ranar 31 ga watan Junairu, 2023 ne ranar karshen amfani da tsaffin takardun kudin N500, N200 da N1000.

Ekefiele
Ko Sambisa Mun Tura Ma'aikata Su Canzawa Mutane Tsaffin Kudi, Emefiele
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Jarumi Abale Zai yi Wuff da Santaleliyar Budurwa, Kati da Hoton Amarya Sun Bayyana

Ba Zamu Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Ba, Emefiele

Emefiele ya ce ko shugaba Buhari ya amince kwanaki 100 da aka bada don mutane su canza kudadensu ya isa.

Ya bayyana cewa har dajin sambisa akwai kudi saboda sun tura jami'ansu su taimaka wajen canzawa mutane kudaden.

Yace:

"Zamu nuna muku bidiyon ma'akatanmu inda suka canzawa mutane kudi in garuruwanmu."
A wurare irinsu Baga, Monguno, Rann, Ngala, Banki, Kirawa, Ngoshe, boda kamaru, Gwoza, Bama, Chibok, Damboa, Isge, Askira, Pulka, duk a sambisa ma'aikatanmu na canzawa mutane tsaffin kudi zuwa sabbi."
Saboda haka nan da ranar 31, duk surutan da wasu ke yi cewa ba zasu iya canza kudin ba. Jama'a Wadanda ke koke-koken nan ba talakawa bane.

Majalisa ta yi fito-na-fito da Gwamnan CBN, tace wajibi ne a dage wa'adin Naira

A wani labarin kuwa, Sanatocin Najeriya sun yi ittifakin cewa ba zata sabu ba, dole ne a gwamnan bankin CBN ya wa'adin ranar daina amfani da tsafiin takardun Naira.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wajibi Ne A Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Da Wata 6: Majalisar Dattawa Tayi Ittifaki

Sanatocin a yau ranar Talata sun bayyana cewa a canza ranar daina amfani da kudin daga ranar 31 ga Junairu zuwa 31 ga Yuli, 2023.

Wannan shine karo na biyu da yan majalisan zasu bukaci gwamnan na CBN ya sauya shawara saboda sabbin kudaden basu isa wasu wurare ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel