Yan Bindiga Sun Harba Bama-Baman Roka a Wani Gari a Zamfara
- Yan bindiga sun kai sabon hari da bama-bama roka da gurneti kan mutanen garin Birnin Magaji a jihar Zamfara
- Wata majiya daga cikin jami'an tsaron Yan Banga yace babu wanda ya mutu ko ya samu rauni a harin
- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an 'yan banga ne suka tarbi maharan aka yi musayar wuta
Zamfara - Yan bindigan jeji sun harba bama-baman roka a garin Birnin Magaji, hedkwatar ƙaramar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Garin Birnin Magaji ya haɗa iyaka da yankuna masu Hatsari na ƙaramar hukumar Batsari, a jihar Katsina mai makoftaka da Zamfara duk a arewa maso yamma.
Wani shugaban yan Banga, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya sahida wa jaridar cewa yan bindigan sun fara da farmakan Manoma a gonakinsu, kilo mita kaɗan a gabashin garin.
Shugaban yan bangan ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Yayin da manoma suka tsira lami lafiya, dakarun yan banga da suka shirya muka bi su aka fara musayar wuta, maharan suka kira a karo musu mutane saboda sun fahimci yan bangan a shirye muke."
"Babura suka iso ɗauke da yan ta'addan suka fara harbo gurneti inda mu ke, Gurnetin bai je wurin mu ba, ɗaya daga ciki ya fashe ya haƙa rami babba a kusa da Rafi. Babu wanda ya mutu ko ya samu rauni har muka kore su."
"Ya zama al'ada a wurinmu yan banga mu zamaa shirye da makaman mu saboda ko da yaushe yan bindiga ka iya shigowa. Washe gari muka gano ɗayan Gurnetin muka kai fadar sarki domin bincike."
Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan Zamfara, SP Muhammad Shehu, ta wayar tarho ba'a same shi ba don jin ta bakinsa game da harin, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Yan sanda sun kama masu kaiwa yan bindiga makamai
A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Kama Makamai a Zamfara, Sun Gano Mutum Biyu Da Ake Zargi
Rundunar yan sanda tace dakarunta sun cafke wasu mutane biyu dauke da Alburusai 325 a kan Titin Gusau-Wanke-Dansadau.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yace sun samu wannan nasara ne bayan samun wasu sahihan bayanan sirri game da safarar makamai daga jahar Benuwai zuwa sansanin 'yan fashin.
Asali: Legit.ng