Gwamnatin Buhari Tafi Ta Obasanjo Nesa Ba Kusa Ba Inji Wata kungiya

Gwamnatin Buhari Tafi Ta Obasanjo Nesa Ba Kusa Ba Inji Wata kungiya

  • Wata Kungiya mai rajin kare murdadun shugaba Muhammadu Buhari a kafafen intanet ta zargi Obasanjo da kasa tabuka komai
  • Shugaban Kasan da a gwamnatinsa aka samu gazawar tattalin arziki da kaso 8, shine zai kuma ce wani ya gaza
  • Ba'abinda yan Nigeria zasuyi ce da shugaba Buhari sai san barka kan yadda ya bunkasa tattalin arzikin kasar nan sosai da sosai.

Abuja - Wata Kungiya mai rajin kare shugaba Buhari a kafar Internet BMO, ta shawarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan ya yarda gwamnatin shugaba Buhari ta fi tasa yiwa Nigeria komai.

Kungiyar tace wannan gwamnati tayi abin a yaba wajen bunkasa tattalin arzikin Nigeria sosai da sosai, duba da yadda tattalin arzikin Nigeria ya habaka yadda hatta kasashen duniya na yabawa Buharin kan yadda ya bunkasa tattalin arzikin.

Kara karanta wannan

Haren-haren da ake kaiwa cikin daji mata da yaran Fulani kawai ake kashewa, Gumi

A wata Sanarwa da shugaban kungiyar ya sanyawa hannu, Niyi Akinsiju da kuma sanya hannun sakataren kungiyar Madueke kungiyar tace ya kamat tsohon shugaban yasan bai bunkasa tattalin arzikin Nigeria ba.

Obj/Buhari
Gwamnatin Buhari Tafi Ta Obasanjo Nesa Ba Kusa Ba Inji Wata kungiya Hoto: UCG
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Yana cewa Buhari bai yi komai ba, kuma bai san yanayin tattalin arzikin kasa ba, alhalin yana cikin wanda suke fi kowa cin gajiyar bunkasa tattalin arzikin da shugaban Buhari yayi"

Mutumin da a gwamnatinsa fa aka samu gazawar tattalin arziki da kaso 8 a farkon da kuma faduwa da kaso 7.35 bayan yayi shekara biyu, sannan kuma a shekarar 2003 yakai kaso 6.59 in aka hada 8 kenan.

sannan kan ya sauka sai tattalin arzikin kasar nan ya tabarbare da kusan kaso 200 bisa yadda ya sameshi. Rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Gwamnan Barno Yakoka Kan Yadda Sabbin Kudin Da CBN, Ya Shigo Dasu Basa Zagayawa A Tsakanin Al'ummarsa

Buhari ya bunkasa sauran fannoni ba iya noma ba kawai

Mai ya barwa Nigeria in banda matsaltsalun man fetir da lalata dukiyar al'umma da kuma rashin wani aikin raya kasa, inji shugaban kungiyar.

Yace Buhari ya bunkasa harkokin noma da kiwo, hadi da hanyoyin samun kudin shiga, zuba jari da kuma wasu hanyoyin da suke kawowa Nigeria kudin shiga.

Abinda yan Nigeria ke fada fa akan mulkinka shine yadda ka kwashe kudinsu kaje kai bunkasa nomanka a gonarka da kayi a garinku.

Jaridar Headtopics ta rawaito cewa kungiyar itace irinta ta farko da aka fara kafawa dan kare muradin shugaban kasa a kafar intanet.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida