Majalisa Za Ta Zauna Shugabannin Bankunan Kasar Nan Don Magance Karancin Sabbin Naira
- Majalisar dokokin Najeriya na neman shugabannin bankuna don tattaunawa dasu kan karancin kudi da ake fama dashi a bankuna
- ‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana kokensu ga yadda babu wadatattun kudade a kasa a kasar, kamar yadda ake tsammani
- Ya zuwa yanzu dai CBN ya ce babu gudu babu ja da baya game da wa’adin da ya sanya na daina amfani da tsoffin Naira
FCT, Abuja - Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da samun karancin kudi a bankunan kasar nan, majalisar dokokin kasa ta yi yunkurin samar da mafita.
Majalisar ta gayyaci shugabannin bankuna a kasar nan don ba da bahasin dalilin da yasa ba a samun sabbin takardun Naira da aka buga a banki, BBC Hausa ta ruwaito.
A cewar rahoton da muka samo, an ce shugabannin bankunan za su bayyana ne a gaban majalisar a ranar Laraba 25 ga watan Janairun da muke ciki.
Ganawar za ta kasance ne tsakanin kwamitin majalisa kan bakuna karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado-Doguwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ana neman mafita ga matsalar kudi a Najeriya
A bangare guda, majalisar ta yanke shawarin gayyatarsu ne domin tattaunawa don samu mafita ga karancin kudin da ake samu a kasar.
Hakazalika, rahoto ya bayyana cewa, daga baya za a gayyato shugabannin CBN domin su ma su ba da bahasi game da halin da ake ciki.
Game da wa’adin mayar da tsoffin kudade kasar, majalisar ta kuma bukaci CBN ya kara wa’adin zuwa karshen watan Yulin bana.
'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan karancin kudi
‘Yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da yadda bankuna ke da karancin sabbin kudade bayan kaddamar dasu.
CBN ya sha bayyana cewa, laifin bankuna ne, domin akwai wadatattun kudade a kasa, bankunan sun ki zuwa su dauka.
Idan baku manta ba, a shekarar da ta gabata ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kirkiri sabbin takardun N200, N500 da N1,000 tare da bayyana lokacin da za a daina amfani da tsoffin kudaden.
Har ya zuwa yanzu, bankuna na ci gaba da ba da tsoffin kudade a injunan ATM a wasu yankunan kasar nan.
Wa'adin da CBN ya bayar na mayar da tsoffin kudade dai har yanzu na nan a ranar 31 ga watan Janairun wannan shekarar.
Asali: Legit.ng