Ma'aikatan NAHCO Sun Tsula Tsiya, Sun Hana Jiragen Sama Tashi a Legas Saboda Dalili 1

Ma'aikatan NAHCO Sun Tsula Tsiya, Sun Hana Jiragen Sama Tashi a Legas Saboda Dalili 1

  • Ma'aikatan kamfanin kula da sufurin jiragen saman Najeriya, NAHCO, ya shiga yajin aiki a ranar Litinin, 23 ga watan Janairun 2023
  • Ma'aikatan kungiyoyin da ke karkashin NAHCO sun tafi yajin aiki wanda hakan yasa jiragen sama na kasa da kasa suka kasa tashi ko sauka a Legas
  • An ga fasinjoji masu yawa suna ta yawo da kayansu a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas inda suka makale

Legas - Kamfanin kula da sufurin jiragen sama na Najeriya, NAHCO, ya fada yajin aiki kan rashin karin albashi, ya hana jiragen sama sauka ko tashi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Litinin.

Filin jirgin saman Murtala Muhammad
Ma'aikatan NAHCO Sun Tsula Tsiya, Sun Hana Jiragen Sama Tashi a Legas Saboda Dalili 1. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

A bidiyon da jaridar TheCable ta gani, fasinjoji masu tarin yawa sun rasa gaba sun kasa baya inda suke yawo da kayansu a filin jirgin saman.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Shiga Rudani Yayin da Gangamin APC Ya Zo Karshe Ba Zato Ba Tsammani

A daya bangaren, Oluwatosin Oladeinde, CEO na Money Africa a wallafar da tayi a shafinta na Twitter, tace:

"An hana jiragen sama sauka ko tashi a filin jirgin sama na Legas. Babu tashi sannan basu saukar jirage a yanzu, fasinjojin da za su yi tafiya sun makale."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ma'aikatan da ke yajin aikin na bukatar karin albashi da sauran kayayyakin walwal. NAHCO ta garzaya kotu tun a baya domin neman umarnin hana ma'aikatan tafiya yajin aiki.

Jami'in daya daga cikin kungiyoyin da ke filin jirgin saman, ATTSSSAN, ya tabbatar da yajin aikin ga Channels TV amma yace ma'aikata ne suka tafi yajin aikin ba kungiyar ba.

Kungiyar NUATE kuwa tun a makon da ya gabata ta fitar da takarda inda ta umarci mambobinta da su janye ayyukansu daga filin jirgin saman.

"A saboda haka, dukkan ma'aikatan NAHCO ana umartarsu da su janye ayyyukansu daga ranar Litinin, 23 ga watan Janairun 2023. Wannan lamarin yana da lokaci amma har sai sakatariyoyin kungiyoyin sun bada umarni."

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mai Hannu a Harin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja, An Gano Abu 3

- Wani bangare na takardar yace.

Duk kokarin da aka dinga yi don jin ta bakin mai magana da yawun NAHCO ya gagara yayin da ake rubuta wannan rahoton.

Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya makale a dokar daji

A wani labari na daban, wani jirgin kasa da ya kawo fasinjoji daga Warri zuwa Itakpe ya lalace a tsakar dajin jihar Kogi, lamarin da ya firgita fasinjojin.

Tuni hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta hanzarta kai motoci inda aka kwashe fasinjojin gudun abunda ka iya kaiwa ya kawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel