Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashi Kan Wasu Rukunin Ma'aikata

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashi Kan Wasu Rukunin Ma'aikata

  • Batun karin albashi dai yazo karshe, yanzu haka gwamnatin tarayya ta amince a karawa wasu ma'aikata albashi
  • Tun shekarar 2020 gwamnatin tarayya ta amince da mafi karancin albashi amma abin ya ci tura kawo yanzu
  • Bama karin albashi ba, akwai ma'aikatun da ba'a iya biyansu a wasu daga cikin jahohin Nigeria

Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da zartar da mafi karancin albashi da kuma karin albashin a takanin ma'aikatan hukumar kula da tashohin jiragen ruwa NPA

Mu'azu Sambo wanda yake ministan ma'aikatar sufuri ne ya fadi hakan a wani taro da aka shirya na ma'aikatan a jihar Lagos, wanda akai dan girmama ma'aikatan da sukai aiki tsawon shekara ashirin a hukumar.

A waccar dai shekarar ne dai ministan kawadgo da kula da albashi ya sanar da za'a karawa ma'aikatan albashi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Barno Yakoka Kan Yadda Sabbin Kudin Da CBN, Ya Shigo Dasu Basa Zagayawa A Tsakanin Al'ummarsa

Ministan yace gwamnatin tarayya, ta amince ne da karawa wasu ma'aikatu kawai albashinsu ba dukan su ba. Rahotan The Cable

Amma a wannan taron da akai ran Asabar din nan ministan yace an amince da wannan karin sabida namijin kwazon da shugaban hukumar Bello Koko yayi.

Ministan ya yabawa hukumar kan namijin kokarinta na bunkasa tare da inganta aikinta a koda yaushe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Minista
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashi Kan Wasu Rukunin Ma'aikata Hoto: UCG
Asali: UGC

Ma'aikatar NPA na cikin wanda suka fi kawo kudin shiga

Ministan yayi da yake jawabi ga mahalarta taron yace:

"Ina mutukar jin dadi dadin yadda shugaban wannan hukumar wajen kawo kudin shiga ga gwamnatin tarayya"

ministan yace:

"Shugaban hukumar ya bukaci ne dana tai maka masa wajen habaka tare da bunkasa yadda yadda hukumar ke gudanar da aiyukanta, ciki kuwa harda karawa ko kuma duba yiyiwar karin albashi"

Kara karanta wannan

Alkawura 3 da Shugaba Buhari yayi kuma bai cika ba, SERAP

Ministan ya ci gaba da cewa:

"Ina taya wannan ma'aikatan wannan hukumar wajen karin albashi da suka samu yau, kuma na tabbata zai taimaka wajen bunkasa aiyukansu."

A nasa bangaren kuwa shugaban hukumar, ya godewa gwamnatin tarayya sabida wannan abun da tai musu gami da kara musu albashi da tayi.

Karin Albashi

Tun shekarar 2020, gwamnatin tarayya ta bukaci da gwamnatocin jihohi da su zatar da mafi karancin albashi na N33,000 a jihohin su.

Amma zuwa yanzu jihphin da suka zatar da tsarin basu fi a kirga su ba, sannan har yanzu akwai jihohin da suke bin bashin albashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel