Wasu Gurabe Guda Uku Da Shugaba Buhari Yai Lam'a A Lokacin Yakin Neman Zabensa

Wasu Gurabe Guda Uku Da Shugaba Buhari Yai Lam'a A Lokacin Yakin Neman Zabensa

  • Wata Kungiya mai rajin kare yan kasa da tabbatar da adalci ta zargi shugaba Buhari da gazawa a gwamnatinsa
  • Kungiyar ta ce shugaban ya gaza samar da wasu abubuwa da yai alkawarinsu, sannan kuma ya gaza yakar cin hanci da rashawa
  • Kungiyar ta ja hankalin yan siyasa kan su guji abinda baza su iya aiwatarwa ba, ko kuma su guji yin wasu abubuwa wanda suka san sun sabawa doka

Abuja - Kungiyar nan mai rajin tabbatar da adalci a tsakanin yan kasa SERAP, ta gano wasu cin hanci da aka tafaka a ma'akatun ruwa, Lafiya da kuma ilimi, sannan ta roki shugaba Buhari da yai bincike akan ma'aikatun sabida alkawarin da yayi.

Kungiyar ta gabatar da wannan batun ne a lokacin da take zantawa da manema labarai kan alkwarurrukan da Shugaba Buhari ya kasa cika su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Shugaba Buhari Tace Ta Kashe Sama Da Dala Biliyan Daya Wajen Yaki Da Boko Haram

Kungiyar tace:

"Gwamnatin Buhari ta gaza wajen yakar cin hanci da rashawa, girmamma doka da oda, samar da abubuwan more rayuwa da sauran abubuwa da ya kamata ace gwamnatin tayi ko ta dau alkawarin yi."

Karuwar matalauta a Nigeria

Na daga cikin abubuwan da Buhari yas ha alwashin magance cewa shine yawan mataulauta a Nigeria.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma a wani rahoto da da hukumar kiddiga ta kasa NBS, ta fitar ya nuna yadda sama da yan Nigeria miliyan 133 ke cikin kangin talauci.

Buhari
Wasu Gurabe Guda Uku Da Shugaba Buhari Yai Lam'a A Lokacin Yakin Neman Zabensa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wannan yake tabbatar da yadda shugaba Buharin ya gaza cika alkawarin da ya daukarwa yan Nigeria na fitar da su daga kangin talauci.

Rashin aikin yi

Haka zalika dai hukumar ta fitar da kiddigar yawan marasa aikin yi na karuwa da kasu 22 a kowacce shekara tunda daga hawansa mulki a shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Batun kin bin doka da oda

Kungiyar tace batun ace gwamnati na girmama umarnin kotu wannan batu ne wanda za'a iya cewa sai dai kallo.

Domin akwai umarni da hukunce-hukunce da kotu ta yanke kuma take umartar ita gwamnatin ta aiwatar amma ina, abun ya zama kaman wasan kwaikwayo.

Akwai tarun laifuka da kuma alkwarurruka da gwamnatin shugaba muhammadu buhari tayi zata cika su amma har yanzu da gwamnatin tazo gangara ba'a fara ganin abun da ta fada ba.

Mataimakain daraktan yace:

"Shi yasa muke kira da yan takara na yanzu da suke kokarin neman kujarun da su san abin da zasu fada, kuma sun tabbatar da abinda zasu fadan nan zasu iya aiwatar da shi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel