Yan Ta'adda Sun Sace 'Dalibai 4 A Hanyarsu Na Dawowa Daga Bikin Aure' A Zamfara

Yan Ta'adda Sun Sace 'Dalibai 4 A Hanyarsu Na Dawowa Daga Bikin Aure' A Zamfara

  • Yan ta'adda sun sace wasu daliban kwallejin fasahar Lafiya a jihar Zamfara a hanyar Kaura Namoda - Birnin Magaji
  • Rahotanni sun bayyana cewa an sace daliban ne yayin da suke dawowa daga halartar bikin aure wata kawarsu
  • Kakakin yan sandan jihar Zamfara ya tabbatar da sace matafiya amma ya ce babu tabbas cewa da daliban cikinsu

Jihar Zamfara - An rahoto cewa yan bindiga sun sace wasu dalibai hudu yayin da suke dawowa daga daurin wani abokinsu a kan hanyar Kaura Namoda da Birnin Magaji a Zamfara, rahoton Premium Times.

Wadanda abin ya faru da su da aka ce daliban Kwalejin Fasahar Lafiya ne ta Tsafe, sun halarci daurin auren ne tare da wasu yan uwansu uku da aka sace su.

Taswirar Katsina
Yan Ta'adda Sun Sace 'Dalibai 4 a Hanyarsu Na Dawowa Daga Aure' A Zamfara. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun sace daliban makarantar firamaren gwamnati a wata jihar Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara ya tabbatar cewa an sace wasu mutane a kan hanyar Kaura Namoda da Birnin Magaji a ranar Lahadi.

Shehu ya ce ba zai iya tabbatarwa idan daliban suna cikin matafiyan da aka sace ba duba da cewa ba a samu rahoton sace su ba daga iyalansu ko hukumar makaranta.

Kakakin yan sandan ya fada wa The Cable cewa:

"Na san a ranar Lahadi yan bindiga sun tare hanya sun sace wasu matafiya amma ba mu tabbatar ko dalibai bane domin iyayensu ko hukumar makaranta ba su kai wa yan sanda rahoton cewa an sace dalibansu ba.
"Abin da muka sani shine an sace wasu kan hanyar kuma ba a san wadanda aka sace ba amma mun samu rahoton sace wasu a hanyar Birnin Magaji da Kaura Namoda a ranar Lahadi."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Tafi Har Fada Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Daya A Arewa, Sun Kashe Mutum Daya

Ya kara cewa wannan shine abin da suka sani a yanzu don haka ba zai iya cewa an sace dalibai ko ba a sace ba, amma kwamishinan yan sanda ya tura jami'ai a ceto wadanda aka sace.

Yan Ta'adda sun sace malamin addini a Benue

A wani rahoto, wasu mahara da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace babban limamin cocin Katolika a Benue, Rabaran Fada Mark Ojotu.

Yan bindiga sun yi awon gaba da Ojotu ne a hanyar Okpoga zuwa Ojapo misalin karfe biyar na yamma, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164