Wa’adin CBN: Daga Ranar 25 Ga Wata Zan Daina Karbar Tsoffin Kudi, Dan Kasuwa Ya Magantu
- Wani dan kasuwa a jihar Gombe ya zo da sabon salo yayin da ya bayyana lokacin da zai daina karbar tsoffin kudi
- Alhaji Hassan Yahaya Pindiga ya ce daga ranar 25 ga wata ya yi sallama da tsoffin kudi saboda wasu dalilai
- Gwamnatin Najeriya ta sanya wa'din daina karbar tsoffin kudi daga ranar 31 ga watan Janairun 2023
Babbar Kasuwa, jihar Gombe - Alhaji Hassan Yahaya Pindiga, wani dan kasuwa a Babban Kasuwar Gombe ya zo da wani sabon salon da ya dauki hankalin jama'a a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da jiran karewar wa'adin daina karbar tsoffin N200, N500 da N1,000 nan da 31 ga watan Janairu, Alhaji Hassan ya ce shi zai daina ne a ranar 25 ga wata.
Ya rubuta a allon sanarwa a cikin shagonsa domin kwastominsa su ga matsayarsa game da tsoffin kudi.
Wakilin Legit.ng Hausa ya yi tattali zuwa shagon dan kasuwan don jin dalilin da yasa ya yanke shawarin sabanin wa'adin da Babban Bankin Najeriya ya bayyana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan baku manta ba, gwamnatin Najeriya ta buga sabbin kudade a watan Disamban 2022, ta sanya sabbin dokoki da kuma ka'idoji kafin daina amfani da tsoffin.
Dalilin da yasa nace 25 ga wata ne wa'adi na
Da yanke zantawa da wakilinmu, Alhaji Hassan ya ce yana tsoron abin da zai iya biyowa baya ne daga kwastomominsa, domin ba a yiwa mutane.
Ya kuma bayyana cewa, ya yi hakan ne domin jawo hankalin jama'a su gaggauta kai kudadensu bankuna don gujewa asara.
A kalamans, cewa ya yi:
"Saboda kwastomomin ne ba a iya yi musu a kai. Idan na bari nace zan bari har lokacin ya riga ya yi, karshenta zan dauki kudin na kai banki amma na samu akwai jama'a da yawa, ka ga kenan ba lallai nawa su shiga ba a kan lokaci."
Kwalliya ta biya kudin sabulu, amma muna tsoro
Da aka tambaye shi ko hakan da ya yi ya mutane suna kawo sabbin kudi wurinsa ko kuma yin amfani da katin kudi ko tiransifa wajen biyan kudi, sai ya ce:
"Insha Allahu. Don mun fara gani ma daga yanzu. Muna kasuwa Alhamudlillahi amma dai har yanzu muna tsorace.
"Tsoronmu kuma shine; kwastomomi ba sa zuwan siyan kaya ba kamar da ba. Sakamakon da kowa ya yi cikini zai dauki kudin ne ya kai banki ya dan jira lokaci ya gani."
Ya kamata gwamnati ta kara wa'adi
Da yake bayyana kiransa ga gwamnati, Alhaji Hassan ya nemi gwamnati da ta duba tare da kara wa'adin da ta dauka na daina amfani da tsoffin kudin kasar.
Ya ce:
"Ni dai kiran da zan yiwa gwamnati shine; ina son ta taimaka ta jikan mutane a kai tunda mu nata ne. A kara mana wa'adi kamar na wata daya haka ko biyu."
Ana ci gaba da dar-dar da sabbin kudade, ya zuwa yanzu dai kudaden bogi a kasar nan sun fara yawa, ana damfarar mutane.
Asali: Legit.ng