Shugaba Muhammadu Buhari Ya Iso Abuja Daga Kasar Mauritania

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Iso Abuja Daga Kasar Mauritania

  • Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya ya dawo gida Abuja, babban birnin tarayya daga Mauritania
  • Shugaban kasar ya tafi kasar ta Mauritania ne don halatar zaman lafiya na Afirka
  • A wurin taron an karrama shugaban na Najeriya da lambar yabo ta zaman lafiya

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja daga Nouakchott, babban birnin Mauritania inda ya halarci taron zaman lafiya na Afirka karo na uku, The Punch ta rahoto.

Jirgin mai saukan ungulu kirar Leonardo AW139 da ya dako shi daga filin jirage na Nnamdi Azikwe ya isa Aso Rock kusan karfe 4 na yamma, hakan ya kawo karshen tafiyarsa na kasar waje 2023.

Buhari waving
Shugaba Muhammadu Buhari Ya Iso Abuja Daga Mauritania. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

A Mauritania, shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe fiye da dallar Amurka biliyan daya don kwato yankunan da Boko Haram ta kwace a jihohin Borno, Adamawa da Yobe tun 2015.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Buhari ya magantu kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu kan Boko Haram

Amma, Buhari ya koka cewa har yanzu ba kammala samun cikakken tsaro a Najeriya da Tafkin Chadi ba saboda rikicin da ke Libya, Central African Republic da kuma rikicin Rasha da Ukraine.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma ce zaman kashe wanda da matasan Afirka ke yi tare da rashin jawo su jiki wurin tattauna batutuwa ya bawa kungiyoyin ta'addanci dama su rika janyo matasa cikinsu suna adabar yankunan nahiyar Afirka.

Don haka, ya yi kira ga shugabannin Afirka su mayar da hankali kan cigaban matasa, tare da karfafa musu gwiwa su koyi sana'o'i da dena zaman banza.

An kuma bawa shugaban kasar lambar yabo ta zaman lafiya na Afirka da kasar Abu Dhabi ta bashi, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hotunan Shugaba Buhari Inda Ya Samu Lambar Yabon Wanzar da Zaman Lafiya a Afrika

Shugaban kasar na Najeriya ya kuma gana da jakadar kasar Amurka na yancin addini, Rashad Hussain.

Ya kuma ce akwai wasu mutane da ke amfani da addini don cimma bukatun kansu na siyasa da samun kudi, ya bada shawara a cigaba da ilmantar da al'umma.

Shugaba Muhammad Buhari ya tafi wurin bikin ranar sojoji a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron tunawa da sojojin Najeriya da suka rasu a filin daga.

An yi taron ne na shekarar 2023 a Abuja a ranar Asabar 15 ga watan Janairun shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164