Allah Nagode Maka: Matashiya Ta Fashe Da Kuka, Ta Yi Birgima a Kasa Bayan Ta Shiga Jirgin Sama

Allah Nagode Maka: Matashiya Ta Fashe Da Kuka, Ta Yi Birgima a Kasa Bayan Ta Shiga Jirgin Sama

  • Bayan ta sauka daga jirgin sama, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta haddasa yar dirama a filin jirgi don murnar wannan nasara
  • Ba tare da ta damu da sauran fasinjojin da ke wucewa ba, budurwar ta yi birgima a kasa sannan ta fashe da kuka tana mai godiya ga Allah kan wannan tafiya
  • Bidiyon matashiyar ya yadu a soshiyal midiya kuma ya haifar da martani yayin da jama’a suka taya ta murna

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta tsuma zukata bayan ta sauka daga jirgin sama sannan ta haddasa cece-kuce kan yadda ta yi murnar wannan nasara da ta samu.

Matashiyar wacce ta cika da farin ciki ta zauna a kasa sannan ta ware hannunta a sama tare da godiya ga Allah a kan nasarar da ta samu a tafiyarta.

Kara karanta wannan

Budurwar da tayi Amfani da Kudin Makarantarta Shekaru 3 da Suka Wuce ta Kafa Kasuwancin Ban Mamaki

Budurwa a filin jirgin sama
Allah Nagode Maka: Matashiya Ta Fashe Da Kuka, Ta Yi Birgima a Kasa Bayan Ta Shiga Jirgin Sama Hoto: TikTok/@flawlesslinna2023
Asali: UGC

Matashiyar ta kuma yi birgima a kasa ba tare da damuwa da yadda sauran fasinjoji ke kallonta ba. Sannan ta yi kamar zata tashi sai kuma ta durkusa a kan gwiwowinta da hannayenta a sama kafin ta fashe da kuka.

Ta wallafa bidiyon diramar da ta haddasa a filin jirgin a TikTok sannan ta yi masa take da “Gaba daya abun da nake son fadi shine Allah Nagode maka.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jikin bidiyon, ta rubuta jawabin godiya kamar haka:

“Nagode maka ubangiji. Idan ba Allah ba toh hakan baya nufin komai a gareni.”

Bidiyonta ya samu mutum 300k da suka kalle shi yayin da mutane suka taya ta godiya ga Allah. Sai dai ba a tabbatar ba ko wannan ne shigarta jirgi na farko.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Kara karanta wannan

Ina Jin Yaruka 3: Budurwa Yar Abuja Da ke Kwasan Albashi Rabin Miliyan Tana Neman Mijin Aure, Ta Fadi Irin Wanda Take So

mhizRoyaltybae ta ce:

“Ina tayaki murna yar’uwa kai inama ace zan iya yin wannan ko wani ya yi mun zan yi faaa don ba abu ne mai sauki ba barka da dawowa gida sahiba.”

Lhady ta ce:

“Na taya ki murna Allah abun godiya. Nima Allah ya yi mun irin ta ki Ubangiji ya bude mun kofofin tafiya da kanwata da sunan Yesu.”

Nelonwa ta ce:

“Ni kenan a makon jiya, na shiga jirgin sama a karo na farko kuma na kasance cikin farin ciki har muka sauka, na fahimci yadda take ji.”

KinkyYo ta ce:

“Bari na cinka wannan ne hawan jirginki na farko ko? Na tayaki godiya ga Allah.”

Za a yi yaki: Marowacin saurayi ya shiga firgici yayin da ya turawa budurwarsa N20k har sau biyu

A wani labari na daban, an sha yar dirama tsakanin wata budurwa da saurayinta dan kankamo bayan ya yi kuskure wajen tura mata kudi.

Saurayin dai ya yi niyar tura mata kudi N20,000 ta asusun bankinta amma sai ya yi kuskuren turawa har sau biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel