Yadda Jami'an Kwastam Suka Samo Motar 'dan Majalisa da aka Kwace a Abuja, a Jihar Neja

Yadda Jami'an Kwastam Suka Samo Motar 'dan Majalisa da aka Kwace a Abuja, a Jihar Neja

  • Hukumar kwastam ta Najeriya ta gano motar wani 'dan majalisa daga jihar Ribas, Hon Chidi Frank Nwiyoka da aka sace bayan sa masa bindiga a Abuja
  • Jami'an tawagar hadin guiwar sintiri tsakanin iyakoki (JBPT) suka tare motar mai lamba KUJ 570 MB da ta taso daga Abuja zuwa Kaduna gami da bukatar takardun motar
  • Hakan yasa matukan motar tserewa daji wanda yayin bincikar motar, sun gano wani kati dauke da bayanan 'dan majalisar, wanda daga bisani ya bayyana yadda aka kwace motar

Hukumar kwastam ta Najeriya, yankin tsakiyar Arewa, bangare na 3, Illorin, dake jihar Kwara, ta gano wata mota kirar Toyota Land Cruiser Jeep mallakin wani 'dan majalisa daga jihar Ribas, Hon Chidi Frank Nwiyoka.

Motar 'dan majalisa
Yadda Jami'an Kwastam Suka Samo Motar 'dan Majalisa da aka Kwace a Abuja, a Jihar Neja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An ruwaito yadda barayi suka sace motar a bayan sanyawa matukin bindiga a cikin Abuja shekarar da ta gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an hukumar sun bayyana yadda suka kama motar mai lamba KUJ 570 MB daga Abuja tana kan hanyar zuwa Kaduna, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Joint Border Patrol Team (JBPT) tawagar hadin guiwar sintiri tsakanin iyakoki da aka tura yankin Suleja cikin jihar Neja suka bukaci a gabatar da takardun motar daga wasu biyu da ke kan motar.

"Sai dai sun nuna kamar waya suke da mai motar gami da tserewa cikin daji suna masu watsi da motar.
"Yayin bincike, jami'an sun gano wani kati da ke bayyana bayanan 'dan majalisar, Chidi Nwiyoka, wanda daga bisani ya ce an kwace motar daga direbansa bayan sanya masa bindiga a wuraren yankin Gwarimpa na Abuja, yayin da aka tuntubesa.
"Da zarar an samar da takardun motar ga jami'an kwastom din, sannan an tabbatar da sahihancinsu, yankin zasu mika motar da 'yan sanda don cigaba da bincike da gano yadda aka saceta."

- Shugaban JBPT, Olugboydgs Peters, ya bayyana yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin game da al'amuranta na shekarar da ta gabata, kamar yadda jaridar ThisDay ta rahoto.

Kotu ta aikewa Emefiele kiran gaggawa, tace ya bayyana a gabanta

A wani labari na daban, kotun tarayya da ke a Abuja ta yi kira ga gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Hakan ya biyo bayan maka shi a kotu da kamfanin Linas yayi kan rike musu kudin bashin Paris Club da yayi ya ki biya duka da an yi masa umarnin biyansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel