Jirgin Sama Ya Fado Kan Makarantar Yara a Ukraine, Minista da Mutum 15 Sun Mutu
- Wani mummunan lamari ya faru a kasar Ukraine, inda ministan harkokin cikin gida ya kwanta dama
- An ruwaito cewa, hadarin jirgin sama ya yi sanadiyyar mutuwar ministan da wasu mutane 15 a wata makaranta
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ta Ukraine ke ci gaba da fafata yaki tsakaninta da makwabciyarta Rasha
Kyiv, Ukraine - Akalla mutane 16 ne suka mutu, ciki har da kananan yara da ministan cikin gida na Ukraine yayin da jirgi ya fadi a kusa da wata makarantar a wajen birnin Kyiv.
Wannan na fitowa ne daga hukumomin kasar a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023, inji rahoton Channels Tv.
Shugaban ‘yan sandan kasar, Igor Klymenko ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tabbas hadarin ya hada ministan cikin gida Denys Monastyrsky.
A bidiyon da ya yadu na bayan faruwar hadarin, an ji mutane na kuka yayin da wuta ke cin jirgin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Halin da ake ciki
Ya zuwa yanzu dai an ce an kwantar da yara 10 a asibiti kasancewar sun samu raunuka masu yawa a jikinsu, rahoton Reuters.
An nada Monastyrsky mai shekaru 42 da ‘ya’ya biyu a matsayin ministan harkokin cikin gida na Ukraine a 2021, kamar yadda rahoto ya bayyana.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa, a lokacin da jirgin ya fadi, yara da ma’aikatan makarantar na karatu a makarantar. Tuni aka kawo likitoci da ‘yan sanda don kawo dauki.
An ce wurin da lamarin ya faru yana nan kusa da yankin Brocary ne mai nisan mil 12 da Arewacin birnin Kyiv.
Rikicin Rasha da Ukraine
Idan baku manta ba, sojojin Rasha da Ukraine sun tafka yaki yaki don mallakar Brovary a farkon mamayar Moscow har zuwa lokacin da sojojin Rasha suka janye a farkon watan Afrilun bara.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya tura rundunar sojin kasarsa zuwa yankin Yammacin Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun bara.
Faduwar wannan jirgin dai na zuwa ne bayan da wani harin makamin Rasha ya kashe mutane 45 ciki har da yara shida a birnin Dnipro a karshen mako.
Jirgi ya fadi a kasar Nepal
Ana yawan samun hadurran jirgi a duniya, a makon jiya ne wani jirgin fasinjoji a kasar Nepal ya fadi.
Rahoton da muka samo ya nuna bidiyo da hotunan yadda jirgin ya fadi a lokaicn da yake shirin sauka.
An ruwaito cewa, jirgin na dauke da mutane 72 ne a lokacin da lamarin ya faru.
Asali: Legit.ng