Sama Da Naira Biliyan Dari Hudu Da Doriya Muka Kashe Wajen Yakar Boko Haram

Sama Da Naira Biliyan Dari Hudu Da Doriya Muka Kashe Wajen Yakar Boko Haram

  • Wasu matsutsan kudade gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tace ta kashe wajen yaki da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram
  • In Ka canja kudin zuwa Naira ya kai kusan kimanin Naira biliyan dari hudu da doriya a kudin Nigeria
  • Shugaban yace kudaden an kashesu ne dan siyan kayan aiki da kuma inganta hanyoyin da dabarun yaki da yan ta'addan

Murtaniya - Shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta kashe sama da dala biliyan daya wajen siyo kayan aikin yakar boko haram a yankin arewa maso gabas

Shugaba Buhari yace:

"Lokacin da na karbi mulkin Nigeria a shekarar 2015, yan kungiyar Boko Haram sun kusan mamaye daya bisa uku na jihar Barno, da wasu bangarori na jihar Yobe da kuma wasu kananan hukumomim mulki da suke hannunsu"

Shugaba Buhari na wannan jawabin ne a wajen taron zaman lafiya na kasashen Africa da ake gudanarwa a Murtania

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Buhari ya ci gaba da cewa mun samu damar kwato wadannan garuruwan da kuma wasu gurabe da suka kwace.

Shugaba Buhari yace mun samu damar zuba zunzurutun kudi sama da dala biliyan daya wajen samar da makamai da kayan aikin da za'a yaki wadannan yan ta'addan tun daga 2015 har zuwa yanzu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari
Sama Da Naira Biliyan Dari Hudu Da Doriya Muka Kashe Wajen Yakar Boko Haram Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Channels Tv ta rawaito ta samu kwafin wannan takardar da mai magana da yawun shugaba kasa ya sanyawa hannu da take cewa shugaba Buhari zai ci gaba da hada karfi da karfe da sauran kasashen da suke makotantaka da su wajen ganin an kawo karshen matsalar

a yayin taron dai an karrama shugaba Buhari da lambar girmama ta Abu Dhabi dan himmarsa wajen bukasa zaman lafiya a Nigeria

Buhari yace ya kamata a dubi kasar Libya

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Wike Ya Yi Sabuwar Magana Kan Wanda Zai Goyi Baya a 2023

Shugaba Muhammadu Buhari yace ya kamata ace zama ko taron da za'ai na gaba, kasashen Africa suyi duba na tsanaki kan abubuwan da suke faruwa a kasar Libya da kuma samar musu da mafaka.

Shugaba Buhari yace:

"Akwai san rai da kuma san zuciya ga wasu kasashe da suke nunawa kan kasar Libya, wanda shine dalilin kin kawo karshe tashin tashinan nan"
"Indai ana so ai maganin wannan matsalar to dole ne a dubi kasar sannan asan abun da ya kamata ayi akanta"

Shugaba Buhari ya kara nanata kudirin gwamnatinsa wajen bada hadin kai dan ganin an samu kulla alaka a tsakaninsa da kasashen African wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a tsakaninsu.

Shugaban kuma ya roki sauran shugabannin kasashen Africa da suka halarci taron da su aiwatar da abinda suka koya ko aka basu shawara kan zaman lafiya ko kuma daga sauararon bayannan da shugaban kasashen sukai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel