Wasu Mutane Na Fake Wa da Addinin Domin Cimma Burin Siyasa da Arziki, Buhari
- Shugaban kasar Najeriya ya bayyana cewa wasu mutane na shiga inuwar addini don cimma burinsu kan tattalin arziki ko siyasa
- Shugaba Buhari ya bayyana wata tattaunawa da ya yi da tsohon shugaban Amurka, Donald Trumph, a fadar White House
- Shugaban kasa Buhari ga samu lambar yabo kan zaman lafiya a ziyarar da ya kai kasar Muritaniya
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yace akwai wasu mutane dake fakewa Addini domin cimma kudirinsu na Arziki da kuma siyasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasa ya bayyana haka ne ranar Talata a birnin Nouakchott na kasar Mauritania yayin ganawa da Rashad Hussain, Ambasadan US na kungiyar yancin Addini ta kasa-da-kasa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adedina ya fitar, Buhari yace akwai bukatar mutane su tashi su cigaba da neman ilimi ta yadda ba wanda zai yaudare su.
Mun taba magana kan haka a White House - Buhari
Shugaban Najeriya ya ba da labarin wata ganawar sirri da ya yi da tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a White House, ya tuna lokacin da Trump ya tambaye shi, "Meyasa kuke kashe Kiristoci a Najeriya?"
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Buhari yace ya baiwa Trump amsar cewa "abubuwan dake faruwa a kasar ba shi da alaƙa da Addinin, ta'addanci ne da wasu mutane ke shiga rigar Addini don cika burinsu kan tattalin arziki da kuma siyasa."
"Wannan matsalolin da Najeriya ke ta fama da su tsawon shekaru duk ba su kamata ba. Wasu ne ke fakewa da Addini amma sakamakon inganta ilimi, mutane sun fara fahimta."
"Mafi yawan mutane suna son yin Addininsu ba tare da katsalandan ba amma wasu yan jari hujja suna amfani da ɗan sabanin addini domin cika burinsu."
"Idan mutane suka samu ilimi, ba zasu lamurci wani ya zo ya gurbata masu tunani ba saboda mafitarsa. Haka idan wasu (yan siyasa) ba su cancanta ba sai su fake da kawo uzurirrika ciki harda Addini."
Ambasada Husain yace US na da sha'awar hadin guiwa da Najeriya a bangaren ilimi domin samun zaman lafiya da jituwa tsakanin addinai, Punch ta ruwaito.
Mun gama da Boko Haram - Buhari
A wani labarin kuma Shugaba Buhari yace babu wani yanki dake karkashin kungiyar Boko Haram a faɗin Najeriya
Yayin ziyararsa a kasar Mauritania, shugaban kasan ya ce gwamnatiɓ ta kwato duk wani yanki ko gari da yan ta'addan suka kwace a baya.
Haka nan Buhari ya karyata labarin da ake yaɗawa na kai harin Boko Haram,a cewarsa masu daukar nauyin ya'addan suna son rugaza kasar.
Asali: Legit.ng