Kun Watsar Da Aiyukan Da Suke Wajibi A Gareku Kun Tafi Yawon Kamfe

Kun Watsar Da Aiyukan Da Suke Wajibi A Gareku Kun Tafi Yawon Kamfe

  • Yan siyasa da masu neman mukaman a zaben da yake karatowa sun bazama yawon neman yakin neman a zabesu
  • Da yawa daga cikin yan majalissar dokoki na kasar nan sun bazama ko bin gwamnonin jihohinsu ko kuma yan takarar shugaban kasar Nigeria
  • Hakan ya tsayar da aikin majalissar duk da ta tafi hotun kirsimeti da sabuwar shekara amma bayan dawowarsu ba'a samu yawan yan majalissar da ake bukata dan zartar da hukunci ko kudiri a majalissar ba

Abuja - Majalissar dokokin kasa ta dawo daga hutun sabuwar shekara da kirsimeti a ranar talatar nan, amma majalissar ta kasance da karancin yan majalissar da suka halarci zaman.

Shugaban majalissar wakilan Femi Gbajabiamila ya roki yan majalissar da su bar yakoki ko shirin siyasa da suke, su dawo zaman majalissar.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

A yayin da yake bude zaman majalissar da jawabinsa, Femi yace:

"Ina rokan yan majalissar da suke wannan gidan da su daure su dawo wannan zauran domin shine abun da yan yankinsu suka zabesu suyi ba yakin neman zabe ba"

Yace wasu daga cikin yan majalissar zamansu ya kare a gidan, yana bukatarsu da su daure su karasa aiyukan da aka zabe su akafin zabe. Rahoton The Punch

Sannan yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya kamata mu fara sabuwar shekarar da aiyukan da zasu bunkasa aiyukan wannan gida da kuma abubuwan da zasu kawo yan Nigeria ci gaba da bunkasa"

Jaridar The Cable tace kakakin majalissar ya roki da yan majalissar su dawo majalissar kafin su tafi hotun zabe wanda yake daf da karatowa.

Femi.
Kun Watsar Da Aiyukan Da Suke Wajibi A Gareku Kun Tafi Yawon Kamfe Hoto: UCG
Asali: UGC

Kakakin yace akwai aiyukan da ya kamata ace an kammala su kafin ace an kulle majalissar ko kuma an bada hutun zabe.

Kara karanta wannan

Jerin Matsaloli Jingim da ke Jiran Duk Wanda Zai Gaji Shugaba Buhari a Aso Rock

Mai yasa yan majalissar zasu koma zaman majalissar

Kakakin majalissar yace akwai kudurori masu tarin yawa, da ya kamata ace hukumar ta gabatar da su, sannan kuma akwai wanda za'ai karatu na biyu ko na uku a kansu.

Kuma wadannan kudurorin duka sun shafi ci gaba da bunkasa yan kasa, dan haka nake rokon ku da ku dawo.

Yace yadda muke shan suka a wajen yan Nigeria, bai kamata ace ko da yaushe kuma muna bude kofar da zasu ga baikon mu ba.

Sannan Femin yace:

"Dole ne kuma mu tabbatar da wa yan Nigeria cewa za'ai zabe sahihi wanda suke bukatar samun wanda suka zaba, hakan bazai yiwu ba, dole sai mun zauna mun fito da wasu dabaru da shawarwari kafin gudanar da zaben"

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida