Kungiyar Gwamnonin Nigeria Ta Gayyaci Gwamnan Babban Bankin Nigeria

Kungiyar Gwamnonin Nigeria Ta Gayyaci Gwamnan Babban Bankin Nigeria

  • Emifele ya shiga tsilla-tsilla, gwamnoni na nemansa, jami'an tsaron DSS na nemansa, sannan yanzu kuma kotu ana jiran umarnin kotu akansa
  • Tun bayan da aka fito da batun sauyin kudi da kiuma tsaruka game da kudaden Nigeria, gwamnan babban bankin kasa ya fara shan suka da wasu martani daga yan kasa, kungoyi da sauran al'umma
  • Yanzu dai kungiyar gwamnonin Nigeria karkashin gwamnan jihar Sokoto, ta gayyaceshi dan ya amsa wasu batutuwa da suka shafi bankin

Abuja - Kungiyar gwamnonin Nigeria (NGF) ta gayyaci gwamnan babban bankin Nigeria CBN, Godwin Emefile, wani mitin wanda zata gudanar ta kafar intanet

Zaman wanda aka shirya za'a gudanar a ranar Alhamis din nan mai zuwa, kuma ake sa ran za'a tattauna kan batun sauyin kudi da kuma wasu maganganu masu kama da haka.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai kula da harkokin sadarwa na kungiyar ya ya sanyawa hannu a ranar talatan nan da dadddare. Rahotan Premium Times

Takardar gayyatar gwamnan bankin ta fito ne bisa umarnin shugaban gwamonin Aminu Waziri Tambuwal gwamnan Sokoto.

Emefiele
Kungiyar Gwamnonin Nigeria Ta Gayyaci Gwamnan Babban Bankin Nigeria Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An yiwa zaman taken:

"Tattalin arziki, tsaro da inganta kudin Nigeria"

Kungiyar tace akwai kuma wasu gwamman tambayoyi da gwamnan zai amsa daga wasu kungiyoyi da kuma masu kula ko sa ido kan tattalin arzikin kasa.

Jaridar Tribune tace wannan gayyatar dai na zuwa ne bayan da gwamnan ko bankin ya sanar da sauya kudin kasa wanda suka hada 100, 200, 500, da kuma 1000, sannan bankin ya sanar da daina amfani da tsofin daga karshen wannan watan.

Wasu tsarukan babban bankin kasa kan cire kudi

Kara karanta wannan

Wike Ya Samu Tangarɗa, Gwamnan G-5 Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Yuwuwar Haɗewa da Atiku

Bayan wannan kuma a watan Nuwanban shekarar da ta gabata, bankin ya fito da wani tsari kuma wanda ya kayyade cire kudi ga dai-daiku da kungiyoyi ko kuma masana'antu, wanda yace zai fara aiki a sati na biyu na watan Janairu.

Sabuwar dokar ta sanya yan Nigeria cikin fargaba da zulumin yadda hada-hadar kudi zai kasance musamman ma a wajajen kananun yan kasuwa

To sai dai bayan matsi daga wasu yan kasa, bankin ya kara wa'adin kan wanda ta yanke tun farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel