Jerin Matsaloli Jingim da ke Jiran Duk Wanda Zai Gaji Shugaba Buhari a Aso Rock
- A watan Fubrairu ne INEC za ta gudanar da zaben da zai kawo sabon shugaban kasa a Najeriya
- Akwai kalubale da suke dankare su na jiran duk wanda ya yi nasarar lashe zaben da za a shirya
- Kalubalen da ake tunani za a gada sun kunshi na tattalin arziki, zamantakewa da kuma hadin-kan
Mun jero wasu daga cikin matsalolin da za a cigaba da fuskanta ko bayan an yi sabon shugaba a Najeriya.
Ga wasu daga cikin manyan matsalolin nan kamar haka:
1. Rashin zaman lafiya
Duk da an samu lafawar rashin tsaro a jihohi da-dama, har yanzu ana fuskantar barazanar hare-hare a dalilin tabarbarewar tattalin arziki da bakar siyasa.
2. Hako danyen man fetur
Gwamnatin Najeriya ba ta iya hako adadin danyen man da ya kamata a kowace rana, raguwar adadin a dalilin rashin tsaro yana da tasiri a kan kudin shiga.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
3. Tashin farashin kaya
Akwai yiwuwar a cigaba da fama da tsadar rayuwa har zuwa lokacin da za a rantsar da sabon shugaban kasa, an yi wata da watanni farashi ba su sauka ba.
4. Talauci
Alkaluma su na nuna ana samun karuwar talakawa a Najeriya a halin yanzu. Sabon shugaban kasar da zai hau mulki zai samu mutane miliyan 133 cikin fatara.
5. Rashin ayyukan yi
Baya ga fatara da ake fama da ita, babu mamaki don an ji akwai karancin ayyukan yi a kasar nan. Hakan ya jawo matasa su ke yawon fita ketare.
6. Bashi
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbo aron kudi masu yawa a shekaru bakwai, hakan ya sa wanda zai magajinsa zai yi fama da biyan bashi a mulkinsa.
7. Tallafin man fetur
A wani rubutu da Okechukwu Nnodim ya yi a Punch, ya ce za a gaji matsalar tallafin fetur. Gwamnati ba za ta iya biyan kudin ba, dole fetur ya yi tsada kenan.
8. Farashin Dala
A ‘yan shekarun bayan nan, darajar Naira ta karye sosai a kasuwa. Wanda zai zama shugaban Najeriya zai yi fama wajen rage tsadar Dalar Amurka a kan Naira.
9. Wutar lantarki
Har gobe ana fama da matsalar lantarki a fadin Najeriya, babu mamaki gwamnati mai zuwa ta duba saida kamfanonin raba wutar lantarki da aka yi a 2013.
10. Zaman lafiya
Legit.ng Hausa tana ganin wanda za a mikawa mulki a Mayun 2023 sai ya yi kokari wajen hada-kan ‘yan Najeriya a dalilin rabuwar kai da ya karu sosai a yau.
Tunde Bakare: Ina da takardun gaskiya
An ji labari cewa Tunde Bakare ya nuna bai goyon bayan Bola Tinubu wanda ya doke shi a zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.
A dalilin haka ne Kwamitin neman takarar Tinubu ta caccaki Faston, don haka shi kuma ya samu lokaci ya sake aikawa ‘dan takaran zaben 2023 wani raddi.
Asali: Legit.ng