Yadda Daliba ‘Yar Arewa Ke Sarrafa Ledar ’Pure Water’ Zuwa Kananzir da Man Gas

Yadda Daliba ‘Yar Arewa Ke Sarrafa Ledar ’Pure Water’ Zuwa Kananzir da Man Gas

  • Wata dalibar ajin karshe a jami’ar tarayya da ke Dutse jihar Jigawa, Zaynab Bilyaminu ta gano hanyar samar da kananzir da man gas daga ledojin ruwa
  • Wannan hazikin tunani mai amfani na sauya ledar ‘pure water’ zuwa abu ami amfani wani sashe ne na binciken karshe da dalibar ke yi na kammala karatu
  • Zaynab ta samu karsashin yin wannan binciken bayan da ta gano akwai hanyar da za a bi don samar da mai daga ledar ruwa

Zaynab Bilyamin, wata dalibar ajin karshe a tsangayar ‘Chemistry’ a jami’ar tarayya ta Dutse a jihar Jigawa ta sauya ledar ‘pure water’ zuwa makamashin kananzir da man gas.

Dalibar ‘yar asalin jihar Jigawa ta dauki wannan maudu’in ne domin iya sauya leda mara kargo zuwa mai da za a iya amfani dashi.

Kara karanta wannan

Saboda mutum 1: An dage taron gangamin tallata Tinubu/Shettima a wata jihar APC

A cewar rahoton Daily Nigerian, Zaynab ta kashe N100,000 wajen kammala wannan babban aikin da ta yi.

Matashiya 'yar Arewa ta ba da mamaki, ta kirkiri mai ta amfani da ledar ruwa
Yadda Daliba ‘Yar Arewa Ke Sarrafa Ledar ’Pure Water’ Zuwa Kananzir da Man Gas | Hoto: @OvieNews
Asali: UGC

Yadda Zaynab ta yi wannan aikin

Malami mai kula da binciken da Zaynab ta yi, Aminu Dauda ya magantu kan yadda dalibar tasa ta yi aikin tabbatar da sauya ledar zuwa mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaynab ta ce ta ji karsashin yin wannan binciken ne bayan da ta gano abu ne mai yiwuwa a sauya leda mara amfani don samar da mai.

Wani Ovie Ali ne ya yada hotunan aikin Zaynab a sgafin Twitter, mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali.

Kalli hotunan:

Martanin jama’a

@IamKennyBabs:

“Akwai matsala a kanmu a kasar nan. Za ka zaci gwamnati za ta yi abun kirki a wannan fannin ta hanyar ba da abin da ake bukata wajen sarrafa shara a kasar.”

Kara karanta wannan

Ba a Afrika kadai bane: Kamar dai na ASUU, malamai a Ingila za su shiga yajin aiki

@jhopes_2217:

"Babban lakcara a tsangayarmu ya yi aiki irin wannan, sauya dattin LDPE zuwa danyen mai da kuma mai dashi mai. Man na aiki wajen aikin janareto na awanni.”
"Wannan hanyar sauyin aka kiransa “PYROLISIS.”

@I_am_Blazzer:

"Na ga da yawan mutane anan suna kokarin cewa roba ana samunta ne daga danyen mai.
“Idan duk kun san tsarin...me ya hana ku yi tun tuni.
"Zaynab ta yi abin da injiniyoyi a Najeriya ke nema kuma ya kamata a karfafa mata gwiwa tare da tallafa mata ba nuna mata hali ba anan.”

Hakazar 'yan Najeriya a iya nan ta tsaya ba, an sha samun lokutan da 'yan kasar ke aikata abubuwan ban mamaki.

A halin da ake ciki, kafin saukarsa a mulki, shugaba Buhari zai kaddamar da jirgin sama mai saukar ungulu da aka kera a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.