Jami'ai Sun Damke Mai POS a Zamfara Kan Zargin Hada-hadar Kudi da 'Yan Bindiga
- Jami'an Tsaron Farar Hula, NSCDC, na Najeriya na jihar Zamfara sun yi ram da wani mai POS, mai suna Mustapha bayan gano yadda 'yan bindiga suka yi hayarsa don kasuwancinsu na kudi
- Mustapha ya bayyana yadda 'yan bindigan suka daukesa aikin kasuwancin kudi gami da siya masa na'urorin POS biyu don taimaka musu wurin siyan abubuwan bukatarsu ta hannun shi
- Sai dai, bayan samun labarin yadda jami'an tsaro suka cafkesa, hatsabiban sun yi barazanar halaka mutane uku da suka sace a baya daga ciki harda sarkin yankin
Zamfara - Jami'an Tsaron Farar Hula na Najeriya, NSCDC reshen jihar Zamfara sun yi cafke wani mai POS, wanda aka bayyana sunansa da Mustapha wanda 'yan bindiga suka daukesa aikin kasuwancin kudi.
Kwamandan NSCDC na Zamfara, Muhammadu Muazu, ya ce an kama Mustapha a Birnin Tsaba cikin karamar hukumar Zurmi na jihar, jaridar Punch ta rahoto.
Ya kara da bayyana yadda tawagarsa ta gano na'urorin cire kudi guda biyu daga wanda ake zargin.
Wanda ake zargin ya fallasa yadda shugaban 'yan bindiga ya siya masa na'urorin, yana kasuwancin kudin ne kawai da wadanda ya sani ( 'yan bindiga).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Idan za su siya wani abu kamar miyagun kwayoyi, fetur da kayan abinci, suna aiko wani ne kai tsaye zuwa wurinsaa don karbar kudin duk abun da suke bukata.
"Ko kuma wani lokaci suna umartar mai POS din da kansa yayi amfani da kudin da yake da shi ya siya musu duk abun da suke bukata. Suna kasuwancin ne a boye, sannan da wadanda ya sani kawai yake yi kamar yadda Mustapha ya fallasa.
"Hakan na nuna wannan mutumin kawai an daukesa ne kuma an dauki nauyinsa don yi musu kasuwancin POS.
"Yayin da suka samu labarin cafke wanda ake zargin (wakilinsu) da kuma kwace na'urorin POS din, sun yi barazanar halaka mutane uku da suka sace daga yankin a baya idan ba a basu na'urorin POS din ba ko kuma ma dai, idan ba a saki wanda ake zargin ba."
- Yace.
"Wadanda suka yi barazanar halakawa sune Sarkin Birnin Tsaba da wasu shugabannin jam'iyya. Mai POS din ya dauki lokaci yana sarrafa na'urorin POS biyu, amma yanzu mun bukaci banki su rufe asusun bankinsa.
"Mun shawarci gwamnatin jiha da ta tsaida amfani da POS na wucin gadi, musamman a yankunan karkara.
"Bisa abun da muka lura, wannan zai shafi yadda 'yan bindiga ke amfani da masu POS na kauye don cire kudi. Saboda masu POS din kauye sun fi kusanci da hatsabiban."
- Ya kara da cewa.
Katsina: Sojin sun halaka Kachalla Gudau, kwararren shugaban 'yan bindiga
A wani labari na daban,, jami;an sojin Najeriya sun halaka fitaccen 'dan bindiga, Ibrahim Kachalla Gudau a jihar Katsina.
An gano cewa, yana da hannu wurin halaka jami'an NSCDC bakwai da aka yi a jihar Kaduna a wani farmakin baya-bayan nan.
Asali: Legit.ng