Mahaukaciya Ta Haifi Jariri a Gaban Shagon Wata Mata, Jama’a Sun Shiga Mamaki

Mahaukaciya Ta Haifi Jariri a Gaban Shagon Wata Mata, Jama’a Sun Shiga Mamaki

  • An shiga wani yanayi yayin da aka ga wata mata mai tabin hankali da ta samu karuwar jariri a layi
  • Wannan haihuwa mai ban mamaki ta faru ne a bakin shagon wata mata, wacce tace Allah ne ya turo ta wajenta
  • An ga lokacin da mutane suka taru, suka zagaye mahaukaciyar da ke zaune a kasa, mutane da yawa sun mata kyauta

Wata mata mai tabin hankali ta samu karuwa na wani kyakkyawan yaro a bakin shagon wata mata a kasuwa.

Bidiyon yadda lamarin ya faru ya yadu a kafar sada zumunta, inda aka ga matar na zaune dirsham a kasa ga kuma mutane suna zagaye da ita.

Wasu da ke wurin da ke daukar bidiyo sun shiga mamakin lamarin da sya faru da wannan mata mai tabin hankali.

Kara karanta wannan

Matashi ya Lakadawa Mahaifiyarsa Dukan Kisa Kan Rabon Gado, Tace ga Garinku a Delta

Yadda mai tabin hankali ta haifi jariri a kasuwa
Mahaukaciya Ta Haifi Jariri a Gaban Shagon Wata Mata, Jama’a Sun Shiga Mamaki | Hoto:TikTok/@kwinirene
Asali: UGC

Daga ciki, wata mata ta dauki yaron tare da goya shi kana ta nuna shi da kyau a bidiyon yayin da mutumin da ke dauka ya nemi ganin yaron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'a sun tausayawa mai tabin hankali

Mutane sun ji tausayinta, suka fara tattara kudade domin ba matar mai tabin hankali da jaririnta.

Mata mai shago dai bata fusata ba, cewa ta yi Allah ne ya aiko wannan mahaukaciya domin ta haihuwa a kusa ita.

Ya zuwa yanzu dai Legit.ng bata iya gano ainihin inda lamarin ya faru ba har zuwa lokacin hada wnanan rahoto.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

u9nice Oluwadabira:

"Yaron gas hi lafiyarsa lau.”

benitasamuel615:

"Yaron da aka haifa yau ne kuke dauka haka kuna daura a baya kamar wanda ya kai shekara 1.”

commentking0675:

"Ya kamata ku bincika. Wata kila babansa wani babban dan siyasa ne.”

Kara karanta wannan

Matar Aure Mai Ciki Ta Kama Mijinta Na Sharholiya da Abokiyar Aiki, Bidiyon Ya Girgiza Jama'a

Innocent Ashamar:

"Ina taya ki mirna, hakazalika Allah ya albarkaci dukkan mata, ba za ku lalace ba da yardarm ubangiji.”

ifyfaithchukwuebu:

"Allah sai yaushe gani sai kuka nake ina neman yaro Ya Allah ka albarkace ni. Ina neman tabaurrki da wannan albarkar kafin karshen shekara ka bani nawa jaririn.”

Yadda 'yar aiki ta shafawa jariri HIV

A wani labarin kuma, kunji yadda wata mai renon jariri ta lallaba ta shafa masa cutar HIV ba tare da sanin iyayensa ba.

Bayan wani lokaci, yaro ya kwanta rashin inda daga baya aka gano yana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Mutane da yawa sun yi martani, sun ba da shawarin abin da ya kamata iyayen su yi kan wannan lamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel