Dalilin Da Yasa Najeriya Ke Fama da Rikici Nan Da Can, Gwamna Obaseki

Dalilin Da Yasa Najeriya Ke Fama da Rikici Nan Da Can, Gwamna Obaseki

  • Gwamnan jihar Edo yace rashin tunanin me zamu yi don ɗaga Najeriya ne ya jefa kasar cikin matsaloli
  • Godwin Obaseki ya halarci wurin bikin tunawa da mazan jiya a Benin, yace ya kamata 'yan Najeriya su dau darasi
  • A cewarsa kowane dan kasa tunaninsa mai zai samu daga gwamnati, ba ya tunanin wace gudummuwa zai bayar

Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo yace Najeriya na fama da rikice-rikice ne saboda mutanen ciki tunaninsu kadai me zasu amfana da shi daga gwamnati.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya fadi haka ne a wurin bikin tunawa da mazan jiya wanda ya guda a Benin City, babban birnin jihar Edo.

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki.
Dalilin Da Yasa Najeriya Ke Fama da Rikici Nan Da Can, Gwamna Obaseki Hoto: Philiph Shaibu/facebook
Asali: Facebook

Ya kuma roki 'yan Najeriya su maida hankali wajen samar da dawwamammen zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar nan domin mutunta sadaukarwan da gwarazan mazan jiya suka yi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Sama Cike Da Fasinjoji Ya Yi Mummunan Hatsari, Mutane Da Yawa Sun Rasu

"Yau gamu muna tuna wadan da suka ba da ransu don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai sun samu gindin zama a kasar nan, yana da kyau mu amfana da yau mu yi koyi da sadaukarwarsu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tattalan arziki a kasar nan ya zama abinda ya zama kuma haka ya taimaka wajen angiza wasu daidaiku cikin harkallar manyan laifuka, ya kamata mu magance wannan."
"Ba wai kawai mu tsaya tunanin me zamu amfana da Najeriya ba, mu fara tunanin me zamu yi wa kasarmu, idan har ba zamu yi haka to rikici, rashin tsaro da wahala yanzu muka fara gani."

- Godwin Obaseki.

Gwamnan ya ci gaba da cewa kowa ka gani yana son amfana da Najeriya amma yan kadan ne ke da kokarin yi wa kasarsu hidima.

"Kowa burinsa mai zai samu daga kasa amma kaɗan ne ke tunanin su hidimta wa kasarsu. Mu a Edo sakon da muke kokarin isarwa shi ne bai kamata mutum ya tsaya iya kansa ba mu tafi tare."

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Gindaya Wa Atiku, PDP Sharadi Na Karshe Gabanin Ranar Zabe

A ruwayar Leadership, Obaseki ya yaba wa hukumomin tsaro bisa zaman lafiya da aka samu a jihar, yace gwamnatinsa zata ci gaba da samar nusu kayan aikin don tsare mutane da dukiyoyinsu.

Wike ya sake gargadin PDP

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya sake tunawa jam'iyyar PDP damarta ta karshe ta nemi sulhu da tawagar G-5

Gwamna Nyesom Wike yace har yanzun PDP na da damar neman sulhu da gwamnonin G-5 kafin su bayyana dan takarar da zasu marawa baya.

Wike, jagoran G-5 da ta balle daga PDP yace idan suka rufe kofa, suka zabi wanda suke so, ko sama da kasa zata haɗe ba wanda ya isa ya hana su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262