Jirgin Sama Dauke da Mutane Sama da 70 Ya Yi Hadari, Da Yawa Sun Rasu

Jirgin Sama Dauke da Mutane Sama da 70 Ya Yi Hadari, Da Yawa Sun Rasu

  • Fasinjoji sama da 10 sun rasa rayukansu bayan Jirgin saman da suke ciki ya gamu da Hatsari a kasar Nepal
  • Hukumomin kasar sun bayyana cewa tuni jami'an agajin gaggawa suka zagaye wurin suna kokarin kashe wuta da ceto mutanen ciki
  • Gwamnatin kasar tace Firaminista ya kira taron jami'ansa kan mummunan lamarin da ya faru da Jirgin saman

Nepal - Akalla mutane 16 suka ce ga garin ku nan bayan jirgin sama dauke da mutane 72 ya yi mummunan hadari a Nepal, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Jirgin sama ya taso ne daga babban birnin kasar watau Kathmandu zuwa Pokhara ranar Lahadi yayin da hatsarin ya auku yana kan hanya.

Hadarin jirgin sama a Nepal.
Jirgin Sama Dauke da Mutane Sama da 70 Ya Yi Hadari, Da Yawa Sun Rasu Hoto: leadership
Asali: UGC

Pokhara wani gari ne da ake zuwa yawon bude ido kuma yana da nisan kilo mita 200 a yammacin birnin Kathmandu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

Mai magana da yawun hukumar sufurin jiragen sama, Sudarshan Bartaula, yace mutane 72 ne a cikin jirgin ATR 72 na kamfanin sufurin Nepal’s Yeti Airlines cikinsu har da matuka da yan kasar waje.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna tsammanin kara gano gawarwaki da dama nan gaba," a cewar mai magana da yawun rundunar sojojin kasar.

Wani gidan Talabijin a kasar ya nuna yadda bakin hayaƙi ke tashi daga wurin da hadarin ya faru yayin da ma'aikatan ceto da dandazon mutane suka kewaye wurin.

"Masu kai dauki sun isa wurin kuma suna ci gaba da kokarin kashe wutar da ta tashi, dukkan hukumomi sun maida hankali wajen dakile wutar da kuma zakulo Fasinjoji," inji Gurudutta Dhakal.

Wane hali ake ciki a yanzu?

Gurudatta Dhakal, mataimakin shugaban Kaski ya shaida wa APF cewa yanzun adadin gawarwakin da aka zaro sun kai mutane 29.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

Channels tv ta rahoto shi yana cewa:

"Mun zakulo gawarwaki 29 a halin yanzun kuma mun tura wadanda aka zaro da rai zuwa Asibiti domin a masu magani."

Gwamnati ta kira taron gaggawa

Fira Ministan Nepalz, Pushpa Kamal Dahal, ya kira zaman gaggawa na mambobin majalisar gwamnatinsa domin tattaunawa kan hadarin jirgin a cewar wata sanarwa.

Idan baku manta ba a 2022, wani jirgin sama mallaka Tara Air ya yi hadari mintuna 20 kacal da tashi daga Pokhara da nufin zuwa Jomson.

A wani labarin kuma Jiga-Jigan Jam'iyyar PDP 15 Sun Yi Hadari a Hanyar Zuwa Wurin Kamfe a Filato

Bayanai sun nuna cewa mambobin PDP sun yi hadari ne kafin isa wurin taron bude kamfen dan takarar gwamnan a karamar hukumar Shendam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262