Gobara Ta Tashi A Hedkwatar Yan Sanda Na Kano, Ofisoshi Sun Kone
- Gobara ta lakume wasu ofisoshi a hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya da ke Bompai Kano
- Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta fara ne daga ofishin Provost sannan ta bazu zuwa wasu ofisoshi
- An yi kokarin tuntubar mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa don ji ta bakinsa amma hakan bai yiwu ba
Jihar Kano - An yi asarar dukiya da kaya na miliyoyin naira sakamakon gobara da ta faru a hedkwatar rundunar yan sanda da ke Bompai, karamar hukumar Nasarawa, jihar Kano.
Wani shaidan gani da ido ya fada wa Daily Sun cewa gobarar ta fara ne misalin karfe 2 na ranar Asabar, ya kara da cewa ta shafi ofishin Provost har zuwa ofishin mataimakin kwamishinan yan sanda.
Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost sannan ta bazu zuwa sashin kudi, dakin taro, ofishin kakakin yan sanda, ofishin mai tallafawa kwamishina (bangaren mulki), ofishin mataimakin kwamishina (bangaren mulki) da wasu wuraren.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar shaidun gani da ido, amma gobarar ba ta shafi sabon ofishin kwamishinan yan sanda da wasu gine-gine da ke kallon ofishin ba.
Ana kyautata zaton cewa gobarar ta kona takardu da dama, amma babu rahoton rauni ko rasa rai sakamakon gobarar, kawo yanzu.
Kawo yanzu ba a san dalilin tashin gobarar ba domin ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ba, don ji ta bakinsa.
Amma, jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun samu nasarar kashe wutan, kamar yadda aka gano suna aiki tukuru yayin da jami'an tsaro suka zagaye hedkwatar yan sandan.
Gobara ta yi mummunan barna a hedkwatar yan sanda na Jihar Delta
A wani rahoton, kun ji cewa hedkwatar rundunar yan sanda na jihar Delta a garin Asaba ta kone kurmus yayin da yan sanda suka bazama don tsira da lafiyarsu.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, lamarin ya faru ne sakamakon matsalar wutar lantarki da ya faru a dakin injin sarrafawa, wanda ya haifar da illa ga wasu iloli.
Wata majiya wacce ta nemi a boye sunanta ta ec jami'an hukumar kashe gobara sun isa wurin cikin gaggawa sun kashe wutar.
Asali: Legit.ng