Wuta Ta Lakume Manyan Shaguna 45 a Babban Birnin Jihar Oyo
- Mummunar Gobara ta lakume manyan shagunan sayar da kayan motoci a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
- Babban manajan hukumar kashe wuya na jihar ya tabbatar da cewa akalla shaguna 25 ne Gobarar ta babbake
- Yace jami'am hukumar sun samu nasarar dakile wutar da Asubahin Asabar kuma ba wanda ya mutu
Ibadan, Oyo - Wata maummunar Gobara da ta kama da tsakar dare ta yi kaca-kaca da muhimman kayayyaki na Miliyoyin naira a shahararriyar kasuwar nan, Araromi Spare Parts.
Gobarar ta lakume akalla shaguna 25 da kasuwar wacce ta yi kaurin suna a wajen sayar da kayayyakin safaya dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 2:00 na tsakar daren wayewar garin Asabar sakamakon kona shara a Kasuwar.
Daya daga cikin yan kasuwa masu sayar da kayan Motoci a kasuwar, Olajide Ige, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa wutar ta babbake shaguna kusan 10.
Yanzu-Yanzu: Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma babban Manajan hukumar kashe wuta na jihar Oyo, Canon Akinyinka, wanda ya tabbatar da lamarin ga hukumar dillancin labarai ta kasa, yace shaguna 25 ne suka ƙone.
Akinyinka ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 2:30 na dare daga wani, Mista Soliu kuma nan take ta tura jami'ai kasuwar domin shawo kan wutar.
Ya ce:
"Lamarin ya faru ne sakamakon kona kayan da suka lalace karangatsai babu kula, sun manta basu kashe wutar kona sharar ba kafin su tashi daga kasuwa kuma hakan ya sa ta yadu."
"Bayanan da suka bamu da farko shi ne kusan shaguna 45 gobarar ta taɓa amma lokacin da jami'ai suka dira wurin suka gano Shaguna 25 ne wutar ta babbake."
Ya kara da bayanin cewa jami'ai sun yi nasarar kashe wutar da misalin karfe 5:00 na Asubahin ranar Asabar kuma babu wanda ya rasa ransa sanadin gobarar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yan sanda sun damke makamai a Zamfara
A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Yi Kicibus Da Muggan Makamai a Hannun Wata Mata Da Namiji a Jihar Zamfara
Kakakin yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya ce waɗan da ake zargin sun shiga hannun dakarun 'yan sanda ne ranar 8 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 11:00 na dare.
Shehu ya kara da cewa wadan da ake zargin, Emmanuel Emmanuel da wata mace mai suna, Nana Ibrahim, an kama su dauke da Alburusai 325 da bindigar AK-47 guda ɗaya.
Asali: Legit.ng