Jihohi 8 Da Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Cikin Kwanaki 30

Jihohi 8 Da Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Cikin Kwanaki 30

  • Shugaba Muhammadu Buhari zai taya Asiwaju Bola Tinubu kamfen a jihohi takwas cikin kwanaki 30
  • Bashir Ahmad, hadimin shugaban Buhari kan kafafen yada labaran zamani, ya bayyana hakan
  • A cewar Ahmad, APC ta yi kamfen a wasu jihohi biyu gabanin yanzu amma duk da haka zasu koma

An shirya Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihohi takwas tsakanin ranar 23 ga Junairu da 21 ga Febrairu don kamfen shugaban kasa wa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Bashir Ahmad, hadimin shugaban Buhari kan kafafen yada labaran zamani, ya bayyana shirin tafiyar da shugaban kasan yayi na kamfen a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 14 ga Junairu.

Ahmad ya cewa wannan sabon sauyi ne a yakin neman shugaban kasa na APC da jam'iyyar tayi.

Buhari
Jihohi 8 Da Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Cikin Kwanaki 30
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

A jawabin da ya fitar, yace:

"Sabon Sauyi: Yakin neman zaben shugabancin kasan Tinubu/Shettima da shugaba Buhari zai halarta"

Ga jerin jihohin da Buhari zai halarta:

23/01/23 = Bauchi

30/01/23 = Akwa Ibom

04/02/23 = Nasarawa

06/02/23 = Katsina

09/02/23 = Sokoto

14/02/23 = Imo

16/02/23 = Kano II

21/02/23 = Lagos II Na Karshe

A jerin dake sama, jihohi biyu cikin wadanda shugaba Buhari zai kai ziyara na karkashin ikon jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) yayinda sauran shidan na APC ne.

Hakazalika an nuna cewa APC za ta gudanar da sabon kamfen bayan wanda tayi a baya a jihohin Kano da Legas.

Kano da Legas ne jihohi mafi adadin kuri'u a bisa alkaluman da hukumar zabe ta INEC ta fitar.

Na yi iyakan kokari na kuma ku shaida ne, Buhari Ga Al'ummar Yobe

Kara karanta wannan

Ana Saura ‘Yan Kwanaki Zabe, Rikicin Cikin Gida Yana Wargaza Jam’iyyar APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ziyarar kaddamar da ayyuka da kamfen da ya kai jihar Yobe ya bayyanawa mabiyar jam'iyyar APC cewa ya yi iyakan kokarinsa kuma al'ummar jihar shaidu.

Buhari ya ce gabanin hawansa mulki, rikicin Boko Haram ya addabi al'ummar Arewa maso gabashin Najeriya.

An gudanar taron yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC a Damaturu ranar Talata, 10 ga Junairu, 2023.

Buhari ya bada labarin yadda ya dade yana neman mulki amma bai samu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida