Kwara: Rikici Ya Barke, An Halaka Manomi Tare da Kone Gidajen Jama’a

Kwara: Rikici Ya Barke, An Halaka Manomi Tare da Kone Gidajen Jama’a

  • Rikici tsakanin manoma da makiyaya yayi sanadiyyar rasa ran wani manomi, zubda jini da kuma asarar dumbun dukiya a Eshijiko na gundumar Pada
  • An tattaro yadda lamarin ya auku a daren Lahadi, wanda ya jefa firgici ga mazauna yankin tare da sanya su hijira saboda gudun sake maimaita kansa
  • Ganau ya bayyanawa manema labarai yadda rikicin ya samo asali bayan wani manomi ya tarar da wasu makiya cikin gonarsa da tsakar dare, daga nan ne hatsaniya ta shiga tsakaninsu

Kwara - Wani mutumi ya rasa ransa yayin da wani ya samu matsanancin rauni sanadiyyar rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a Eshijiko na gundumar Pada dake karamar hukumar Pategi a jihar Kwara.

Taswirar Kwara
Kwara: Rikici Ya Barke, An Halaka Manomi Tare da Kone Gidajen Jama’a. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro yadda lamarin da ya faru ranar Lahadi ya bar mazauna yankin da dama cikin firgici, inda da yawansu suka yi hijira daga anguwar saboda tsoron kada harin ya sake maimaita kansa.

Kara karanta wannan

Shahararren Mawakin Najeriya Zai Daina Waka, Zai Zama Makarancin Kur’anin Duniya

Wata majiya da tayi magana game da lamarin ta labarta yadda rikicin ya faru sakamakon wata hatsaniya da ta shiga tsakanin wani manomi, Usman Baba da wasu makiyaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Lamarin ya faru ne sakamakon wani rikici tsakanin wani manomi, Usman Baba wanda ya iske wasu makiyaya a gonarsa da tsakar dare, inda ya umarcesu da su bar masa gona. Al'amarin ya kai ga sa-in-sa wanda ya janyo rasa ran daya daga cikinsu.”

- Kamar yadda majiyar tayi fashin baki.

Wani majiya daga hukumar tsaro ya bayyanawa wakilin Daily Trust yadda mutanen kauyen suka kona Rugar Fulani kurmus, wanda ake zargin sunyi hakan ne don daukar fansa kan kisan manomin da aka yi.

Sarkin Fulanin Illorin ta yamma, Alhaji Idris Ali, ya ce sama da Falani 1,000 sun yi kaura.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

"Matsayarmu bayan samun rahoton kisan manomin shi ne a ba hukumomin tsaro damar yin aikinsu gami da gurfanar da wanda ya aikata laifin. Mun yi mamakin samun labarin yadda suka dauki doka a hannunsu.”

- A cewarsa.

Ta bangarensa, wani sarkin Fulanin Kwara, Alhaji Jao Yahaya, ya ce an tarwatsa gidaje kimanin 500, yayin da daruruwan mutane suka yi kaura.

"An barnata mana ajujuwan makarantar fulani 10, masara, dawa, doya, shinkafa, rogo, babura da shunu masu tarin yawa wadanda zasu kai kimar N50 miliyan sanadin rikicin.”

- Kamar yadda ya shaida.

A cewarsa, karkarar da lamarin ya faru ta kai sama da shekaru 47 da kafuwa, kuma suna zaune cikin lumana da mutane ba tare wani cikas ba.

Yayi kira ga gwamnatin jiha da hukumomin tsaro da su gaggauta kawo musu dauki saboda a yanzu suna fama da rashin muhalli da tsaro a yankin.

Haka zalika, kakakin jami'an kare farar hula gami da tsaro (NSCDC) na jihar Kwara, Olasunkanmi Ayenu, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Tare da bayyana yadda suke lura gami da tabbatar da natsuwa.

Kara karanta wannan

2023: Atiku da PDP Sun Samu Goyon Bayan Manoma Daga Jihohi 7 a Arewa

'Yan ta'adda sun sheke magidanci tare da sace yaransa biyu

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya ta sanar da halakar wani magidanci da yayi artabu da masu garkuwa da mutane.

Bayan halaka shi, sun yi garkuwa da yaransa biyu a yankin Bwari da ke babban birnin tarayya ta Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng