Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Fara Sayar da Fom Din UTME, Ta Fadi Wa’adin Rajista

Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Fara Sayar da Fom Din UTME, Ta Fadi Wa’adin Rajista

  • Hukumar shirya jarrabawar JAMB ta bayyana tsarin da za a bi wajen rajistar jarrabawar UTME na shekarar 2023
  • Hakazalika, hukumar ta bayyana wa'adin da ta debi na UTME da DE a shekarar nan, ta fadi dalla-dalla kwanakin
  • A bangare guda, hukumar ta bayyana abubuwan da ake bukata ga dukkan wanda yake son rubuta jarrabawar

Najeriya - Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta JAMB ta ce ta fara siyar da fom din UTME da DE ga 'yan Najeriya da daliban kasashen waje.

Hukumar ta ce tana gayyatar dukkan daliban da suka cancanta don rubuta jarrawar ta shiga manyan makarantu a zangon karatun 2023 a Najeriya.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da hukumar ta bayyana jadawalin ayyukanta na shekarar 2023 da muka shiga, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Assha: An gurfanar da Tsohon Shugaban ABU Da Ma'ajin Jami'ar Bisa Zargin Aikata Halin Bera, Sun Saci N1bn

Za a fara rajistar JAMB a karshen mako
Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Fara Sayar da Fom Din UTME, Ta Fadi Wa’adin Rajista | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Lokutan rajistar jarrabawar UTME 2023

Lokacin da JAMB ta diba na rajistar UTME a bana ga 'yan Najeriya da ma 'yan kasashen waje zai fara ne a ranar Asabar 14 ga watan Janairu zuwa ranar Talata 14 ga watan Fabrairun bana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba da PIN na rajistar UTME zai kare ne a ranar ta Talata yayin da za a rufe rajistar gaba daya a ranar Juma'a 17 ga watan Janairun 2023.

Lokutan rajistar DE 2023

Game da rajistar DE, ana bukatar mai sha'awa ya mallaki imel kafin fara komai na rajistar.

Za a fara rajistar DE ne a ranar Litinin 20 ga watan Fabrairun 2023 za a kammala a ranar 20 ga watan Afrilun 2023.

Za kuma a yi rajistar ne a ofisoshin JAMB na jihohi ko shiyyoyi a fadin Najeriya, IntelRegion ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam'iyya Ta Maye Gurbinsa

Za a biya biyan kudin JAMB ta hanyar amfani kudin eNaira

A wani labarin kuma, kunji yadda babban bankin Najeriya (CBN) ya hada kai da hukumar jarrabawa ta JAMB tare da bayyana karbar kudin rajista ta hanyar amfani da eNaira.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke kara kaimi wajen kakaba dokar takaita yaduwa kudade a kasar, musamman a shekarar nan.

An kirkiri hanyar biyan JAMB ta eNaira ne domin saukakewa dalibai jigilar biya da kuma kare su dada shiga hannun masu damfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel