Hukumomin Tsaro Sun Kama Tsohon Shugaban Yakin Neman Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP Peter Obi

Hukumomin Tsaro Sun Kama Tsohon Shugaban Yakin Neman Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP Peter Obi

  • A shekarar bara ne dai kotu ta yankewa Doyin Okupe shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP hukuncin Dauri ko zabin tara
  • Bayan yanke hukuncin, da kuma samun bali, an jiyo Doyin na sanar da ajiye shugaban kwamitin yakin neman zaben Peter Obi din
  • A yau dai hukumomi sun sake ram da shi yayin da yake kokarin barin Nigeria zuwa kasar Ingila

Lagos - Tsohon shugaban yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na LP, na kwanan nan Doyin Okupe ya sake fadawa komar jami'an tsaron Nigeria, wanda ake kyautata zaton DSS ne.

An tabbatar da cewa Doyin an kamashi ne a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammad Dake jihar Lagos, yayin da yake kokarin barin kasar nan zuwa Landan. Rahotan jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Kwararan Dalilai 5 Dake Nuna Cewa Wajibi CBN Ya Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira

Doyin
Hukumomin Tsaro Sun Kama Tsohon Shugaban Yakin Neman Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP Peter Obi Hoto: UCG
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me yasa aka kamashi

Yayin da yake zantawa da jaridar PMNewsNigeria, daya daga cikin lauyoyinsa mai suna Tolu Babbalaye yace:

"Jami'an tsaron DSS sun bukaci da ya gabatar musu da takardun da suke nuna ya biya tarar da akai masa a kotu, bayan da kotun ta zarge shi da wawushe wasu kudade a mulkin gwamnatin baya.

Lauyan yace:

"Yaushe wannan cin mutunci zai tsaya? Wai wake son ganin bayan Doyin Okupe, zuwa yanzu fa duk wani zargi da ake masa an ringa da wankeshi, a dan haka nake kira da hukumar tsaron DSS ta saki wanda nake bawa kariya sabida yadda aka tozartashi akaci mutuncinsa, kuma ga rashin lafiya da yake fama da ita".

Laifin da ake zarginsa tun farko

Okupe wanda yake tsohon mai bawa shugaban kasa Goodluck Janathan, an zarge shi da karban kudi kusan N200m daga wajen mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Col Sambo Dasuke mai ritaya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatarwa Da Yan Nigeria Zai Ai Zabe A Watan Gobe Mai Kamawa

A dalilin haka Mai sharia Ijeoma Ojuke ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari ko kuma zabin tara akan laifuka 26 da ake zarginsa da su kuma aka tabbatar masa su.

Lokacin da take yanke hukuncin da hukumar kula da hana ta'annati da dukiyar kasa ta shigar akansa, mai shari'ar tace ta bashi kafin karfe 4:30 na ranar da ya biya tarar ko kuma ta tura shi gidan dan kande dake Kuje.

Nan take dai Okupe ya biya tarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel