Tashin Hankali a Ondo Yayin da Ake Zargin Sojoji Farmakar ’Yan Jam’iyyar PDP
- Jam’iyyar PDP a jihar Ondo ta zargi dan majalisa mai wakiltar Idanre/Ifedore a majalisar kasa, Tajudden Adefisoye da yin hayar sojoji don farmakar mambobinta
- Adefisoye a baya ya yi ikrarin cewa, matasan PDP sun farmaki ayarinsa kuma sun jikkata magoya bayansa a karamar hukumar Idanre ta jihar Ondo
- Da suke martani ga batunsa, shugabannin PDP sun ce farmakar mambobinsu martani ne ga ikrarin taba magoya bayan Adefisoye
Idanre, Ondo - Jam'iyyar PDP a jihar Ondo ta bayyana zargin yadda sojoji suka farmaki mambobinta a karamar hukumar Idanre ta jihar.
Jam'iyyar ta zargi dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Idanre/Ifedore, Tajudden Adefisoye da umartar sojoji wajen aikata wannan aikin illata mambobinta da kuma wargaza wurin taronsu, rahoton Vanguard.
Meye yasa sojoji suka farmaki mambobin PDP?
Jihar Ondo dai na daya daga cikin jiga-jigan jihohin APC, kuma gwamna Rotimi Akeredolu ne shugaban gwamnonin Kudu maso Yamma.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dan majalisar kuma, shine shugaban kwamitin majalisa kan harkokin soja, kuma a baya ya ikrarin cewa, wasu matasan PDP sun farmaki ayarinsa a ranar Asabar 7 ga watan Janairu.
Ya ce harin ya faru a garinsu, kuma an jikkata magoya bayansa da yawa.
A cewar PDP, farmakin da sojojin da tace na bogi ne wani yunkuri na daukar fansa kan harin da aka kaiwa dan majalisar, SaharaReporters ta tattaro.
Martanin PDP ga dan majalisa da APC
Da yake martani game da harin, daraktan yada labarai na PDP a karamar hukumar Idanre, Fasoranti Adeyemi ya yi zargin cewa, abin da sojojin suka yi ya faru ne tsakanin karfe 5:45 zuwa 7:05 na yamma.
Hakazalika, jam'iyyar ta bayyana cewa, an lalata shaguna da kadarorin jama'a, wanda mallakin 'yan PDP ne.
Rikicin APC da NNPP a Kano
A jihar Kano kuwa, rikici ne tsakanin jam'iyyar NNPP mai kayan dadi da kuma jam'iyyar APC mai mulkin jihar.
APC ta bayyana cewa, dan takarar gwamnan NNPP ya sha alkawarin wargaza masarautun Kano guda biyar, zai mai dasu daya kamar yadda suke a shekarun baya can da nisa.
Wannan lamari bai yiwa NNPP dadi ba, domin jam'iyyar ta ce sharri aka yiwa dan takarar, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Legit.ng