APC da NNPP Na Ta Musayar Kalamai Kan Sabbin Masarautu a Kano

APC da NNPP Na Ta Musayar Kalamai Kan Sabbin Masarautu a Kano

  • Jam'iyyar NNPP da APC a jihar Kano na ci gaba da musayar yaw kan yadda aka ce Abba Kabir Yusuf zai rusa masarautun jihar Kano
  • Wannan na zuw ane daidai lokacin da zaben 2023 ke kara matsowa, 'yan siyasa na ci gaba da duba aibin 'yan adawarsu
  • A nasa bangaren, dan takarar gwamnan ya ce babu batun rushe masarautu, karya ce kawai irinta APC mai mulki

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, kalaman dan takarar gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf na rusa sabbin masarautun jihar idan aka zabe shi gwamna na nuni da cewa, zai rusa tsarin da doka ta samar na kacancana daidai da bukatar jama'ar Kano.

Idan baku manta ba, jam'iyyar APC a karkashin gwmana Ganduje ta kirki sabbin masarautu biyar a jihar a 2019, wadanda suka hada da Kano, Bichi, Rano, Karaye da gaya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Ga Atiku, Tinubu Ya Ziyarci Fitaccen Gwamnan G5, Bidiyo da Hotuna Sun Bayyana

Sai dai, a nasa kamfen, Abba Gida-gida ya ce da zarar ya hau gwamna zai rushe masarautun tare da dawo da martabar masarautar Kao guda daya, Vanguard ta ruwaito.

Rikicin APC da NNPP a Kano
APC da NNPP Na Ta Musayar Kalamai Kan Sabbin Masarautu a Kano | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

An bi dokar majalisar dokoki wajen raba masarautun Kano

Da yake martani ga batun dan takarar na NNPP, kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fada a cikin wata sanarwa cewa, kacancana masarautun ya yi daidai da tsarin doka da majalisar dokokin jihar ta samar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Garba ya kuma bayyana cewa, kamar dai kirkirar jiha ko karamar hukuma, kirkirar wadannan masarautu suka zama biyar ya taimakawa ci gaban daukacin jihar Kano.

Ya kuma bayyana cewa, kasa masarautun da aka yi a tun baya ya kawo ci gaba da bayyana, ta fuskar tattalin arziki da fadadar al'adu a yankunan.

Ya kara da cewa, masarautun sun samu karbuwa da goyon bayan mazauna jihar, don haka suke habaka zamantakewa da tattalin arziki jama'a da martaba masarautun gargajiya.

Kara karanta wannan

2023: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar da NNPP Ta Shigar da Dan Takarar APC

Martanin NNPP ga gwamnatin Ganduje

A nasa bangare, mai magana yawun jam'iyyar NNPP, Sanusi Bature ya karyata labarin da kcewa mai gidansa ya furta maganar game masarautun wuri daya.

A kalamansa:

"APC ta rasa ayyukan ci gaba da za ta yi kamfen dasu don a zabe ta, a madadin haka, suna ta maganganun bata suna maras ma'ana.
"Suna son jawo mu cikin musanya marasa amfani, babu inda uban gidana ya yi irin wannan martani game da sabbin masarautu.
"Amma abin takaici cewa Muhammad Garba a matsayinsa na fitaccen dan jarida ya bari ya zubar da mutuncinsa kasa ta hanyar yada labarin karya."

Ba yanzu aka fara wannan cece-kuce tsakanin APC da NNPP ba, kamar yadda rahoton Daily Post ya bayyana.

Babu jituwa tsakanin Ganduje da mabiya bayan Kwankwaso a jihar Kano, hakan na haifar da cikas mai yawa ga tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel