Karancin Mai Zai kai Kusan Wata Shida Inji Hasashen Yan Kasuwar Man

Karancin Mai Zai kai Kusan Wata Shida Inji Hasashen Yan Kasuwar Man

  • A Nigeria duk karshen shekara da sabuwarta yan kasar na fuskantar matsalar man fetir wanda za'a iya cewa ya zama ruwan dare
  • To sai dai a wannan karon matsalar man fetir din ta fara ne tun daga farkon watan takwas na shekarar bara, kuma har zuwa yanzu ba'a daina ba
  • Gwamnatin Nigeria ta maida babban kamfanin mai na NNPC zuwa hannun yan kasuwa da zimmar bunkasa tare da habaka harkokin tattalin arziki a Nigeria

Abuja - Matsaltsalun da abubuwa wanda ba'a tunani sun dabaibaye harkokin samar da makamashin fetir a Nigeria, wanda kuma yan kasuwar man ke cewa matsalar kan iya kaiwa watan Yuni na wannan shekarar.

Harkar mai a Nigeria ta fada garanrambar da ba'a taba ganin irinta ba wanda abubuwa sun dagule mata.

To amma babban kamfanin kasar na mai NNPC, Na ganin matsalar wasu yan kasuwa ne suka janyota. Rahotan The Punch

Kara karanta wannan

Mr Quarong da ake zargi da kashe Ummita Yace Ya Kashe Mata Kudi Kusan Miliyan Sittin

A ranar litinin din nan ministan albarkatun man fetir na Nigeria Timpre Sylva yace kamfanin mai na siyar da man a sara sabida yadda gwamnatin tarayya ke narka kudin tallafin mai a cikin harkar.

Karancin Mai
Karancin Mai Zai kai Kusan Wata Shidda Inji Hasashen Yan Kasuwar Man Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wancan satin ministan kudi da kasafi Zainab Ahmed tace gwamnatin taryya ta ware kudi kusan N3.6trn akan harkokin mai daga farkon wannan shekarar zuwa Yunin wannan shekarar.

Hasashen yan kasuwa masu siyar da mai game da karancin man fetir

Mai magana da yawun yan kasuwa masu siyar da man fetir a Nigeria, Ukadike Chinedu ya fadawa jaridar Leadership cewa kudin tallafin mai da kuma shigo da mai na basu wahala sosai, kuma shi yasa yan Nigeria ke shan wahala

yace:

"Maganar tallafin mai da kuma shigo da shi na cikin dalilin da yasa muke shan wahala wajen samar da wadataccen mai a gidajen mai. kuma wannan matsalar in ba'ayi wasa ba, zata kai har kusan watan yunin wannan shekarar"

Kara karanta wannan

Kishi Kumallon Mata: Wata Mata Ta Kona Kishiyarta Da Wuta Har Lahira

Haka zalika shugaban kungiyar masu bawa yan Nigeria mai, Billy Gills-Harry yace wannan matsalar na cikin abinda ya damesu yake ci musu tuwo a kwarya.

"To a samu abinda za'a siyar mana, shi ya sa muke ta fafutukar neman man, indai an kawo karshen matsalar karancinsa to duk sauran matsalar zata kare"

Asali: Legit.ng

Online view pixel