Gaskiya Ta Fito: An Gano Wanda Ronaldo Ya Siyar da Kofin Ballon d’Or Dinsa Akan £600,000

Gaskiya Ta Fito: An Gano Wanda Ronaldo Ya Siyar da Kofin Ballon d’Or Dinsa Akan £600,000

  • Fitaccen dan kwallon kafa Christiano Ronaldo ya siyar da kyautar Ballon d'Or da ya ci a wasan shekarar 2013
  • An ce wani dan kasar Isra'ila ne ya siya wannan kofin mai daraja, kuma an bayyana me aka yi da kudin
  • Bayan shekaru, an bayyana bayanin mutumin da ya siya kofin da kuma inda aka kashe kudin kofin a duniya

An bayyana waye ne ya siya daya daga cikin kofunan Ballon d'Or da Christiano Ronaldo ya ci a wasanni daban-daban, Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton da ke yawo ya bayyana cewa, wani attajiri dan kasar Isra'ila ne ya lale manyan kudade ya siya wannan kofi mai daraja.

An bayyana yadda aka siyar da kofin mai daraja da Ronaldo ya samu a 2013 ga wani attajirin Ba'isra'ile ta hanyar gwanjon da aka yi a 2017 a kan kudi £600,000.

Kara karanta wannan

Yaro Da Kudi: Matashin Miloniya Ya Siya Motar Marsandi Sabuwa, Ya Dinka Kaya Dauke Da Logon Benz a Bidiyo

An fadi wanda ya siya Ballon D'Or din Ronaldo
Gaskiya Ta Fito: An Gano Wanda Ronaldo Ya Siyar da Kofin Ballon d’Or Dinsa Akan £600,000 | Hoto: goal.com
Asali: UGC

Ronaldo dai ya samu wannan kofi da ake ba gwanayen 'yan wasa har sau biyar, inda ya fara cinsa a 2008 tun yana buga kwallo a Manchester United kafin daga bisani ya koma Real Madrid.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kofin na 2013 da ya samu shine mafi daraja kuma wanda ya sha fama a kai, a lokacin zakarun duniya irinsu Messi da Ribery na kan tashen lashe irin wadannan kofuna.

Ta yaya aka siyar da kofin?

Bayan samun wannan kofi, a lokacin Ronaldo yace zai ba da shi tallafi ga mabukata, Daga nan ne aka yi gwanjonsa a karkashin gidauniyar Make-A-Wish, kuma attajirin Isra'ila Idan Ofer ne ya saye shi.

A cewar wani rahoton jaridar Marca, Ronaldo ya nemi a yi masa kinin kofin na 2013 tare da yin gwanjons, rahoton Mirror.

ESPN kuwa ta ruwaito cewa, ainihin kofin na Ronaldo yana can a ajiye a dakin ajiyar kaututtuka da kofunansa da ke Madiera.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

An ruwaito cewa, kudaden da aka siyar da kinin kofin sun tafi kai tsaye ga gidauniyar tallafawa yara, wanda aka ce za a kashe kan yara masu cututtuka da ke bukatar kula ta musamman.

Wanene Idan Ofer?

A cewar rahoton Forbes, Ofer attajiri ne da darajar kudinsa ya kai dalar Amrka 9.9bn (£8.2bn).

An ce yana da kudade da hannaye da yawa kulob din kwallo guda biyu, inda a baya ya zuba kudinsa Atletico Madrid a 2017.

Daga baya ya zama cikin manyan mamallakan kulob din kwallon kafan kasar Portugal, Famalicao.

Ronaldo dai yanzu ya koma buga kwallo a kasar Saudiyya bayan ya bar buga kwallon a Manchester United.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.