'Yan Ta'adda Sun Kashe Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Da Dan Uwansa, Sun Sace Matan Aure 4 A Kaduna
- Wasu mahara da ake kyautata zaton yan bindiga ne sun kai mummunan hari a kauyen Unguwar Mai Awo da ke Kaduna
- Yayin harin sun halaka ciyaman din kungiyar bada agaji na gaggawa ta Fityanul Islam da dan uwansa, sun kuma sace matan aure hudu
- Wasu majiyoyi daga kauyen sun tabbatar da harin inda suka ce an raunata mutane biyu yayin harin, kuma a halin yanzu suna asibiti
Kaduna - Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe shugaban al'umma kuma mamba na kungiya agaji ta Fityanul Islam a gidansa da ke kauyen Unguwar Mai Awo tare da dan uwansa a Kaduna.
Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu matan aure hudu har da mai shayarwa yayin da suka kai hari a garin da ke kusa da Maraban Jos kan babban hanyar Kaduna-Zaria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi daga kauyen Unguwar Awo sun tabbatar da harin
Lamarin ya faru ne safiyar ranar Laraba kamar yadda majiyoyi daga kauyen suka sanar da Daily Trust.
Wani shugaban matasa wanda ya ce sunansa Adam Unguwar Awo ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya yi bayanin cewa yan bindigan sun bude wuta son tsorata yan kauyen yayin da suka iso garin.
A cewarsa, mutum biyu yan kauyen sun jikkata kuma an kai su asibiti don magani.
Ya ce:
"Yan bindigan sun kashe Malam Ibrahim Abdullahi wanda shugaban al'umma ne kuma ciyaman din kungiyar agajin gaggawa ta Fityanul Islam da dan uwansa Zakari Yau. An kuma sace mata hudu ciki har da mai shayarwa a garin."
Martanin yan sandan Kaduna
Da ake tuntube shi, kakakin yan sandan Kaduna DSP Mohammed Jalige ya yi alkawarin zai bincika ya samu cikakken bayani amma bai bada bayanin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Yan fashin daji sun kai mummunan hari a masallaci a Taraba, sunyi kisa sun sace mutane
A wani rahoton, yan bindiga da adadin su ya kai goma sun kai wani mummunan hari a wani masallaci da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun halaka mutum daya kuma sunyi awon gaba da wani dan kasuwa da yaronsa.
Maharan sun afka wa masallacin da ke mahadar Jalo ne a unguwar Saminaka a birnin Jalingo a lokacin da mutane ke sallar Magrib.
Asali: Legit.ng