Ki Hau Kujera: Hannun Yar Bautar Kasa Ya Gaza Kaiwa Saman Allo, Dalibai Sun Mata Dariya a Bidiyo

Ki Hau Kujera: Hannun Yar Bautar Kasa Ya Gaza Kaiwa Saman Allo, Dalibai Sun Mata Dariya a Bidiyo

  • Wata budurwa da ke aikin bautawa kasa wato NYSC a yanzu ta nuna yadda take gwagwarmaya wajen rubutu a jikin allo
  • Wani bidiyo da Arike ta wallafa a TikTok ya nuna lallai tana matukar wahala wajen rubutu a allon wanda ke sama saboda gajartanta
  • Har ya kai sai da wata daliba ta bata kujera domin ta hau ta yi rubutu, amma ta ki yarda da hakan a bidiyon

Masu amfani da TikTok sun yi martani ga bidiyon wata yar bautar kasa wacce hannunta ya ki kaiwa allon rubutu.

A wani bidiyo da Pretty Arike ta wallafa a TikTok a ranar 9 ga watan Janairu, yar bautar kasar ta ce ta kama aiki a wajen da aka tura ta.

Yar bautar kasa
Ki Hau Kujera: Hannun Yar Bautar Kasa Ya Gaza Kaiwa Saman Allo, Dalibai Sun Mata Dariya a Bidiyo Hoto: TikTok/theprettyarike
Asali: UGC

Arike wacce aka tura makaranta ta shiga aji da wani littafi a hannunta tare da shirin koyar da dalibai.

Kara karanta wannan

Duniya Ba Yarda: Bidiyon Yadda 'Yar Aiki Ta Bata Fuskar Yar Gida, Ta Mata Mummunan Illa

Bidiyon yar bautar kasa tana koyarwa a aji

Sai dai kuma a lokacin da ta so yin rubutu a allo, sai abun ya nuna lallai tsawonta ba zai kaita koina ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tana ta gwagwarmayar ganin ta isa inda take son rubuta darasin da za ta koyar da su amma abun ya gagara har dai ta hakura.

Daliban sun lura da yadda take fama inda suka fashe da dariya.

Sai dai kuma wata daliba ta taimaka mata da kujera don ta hau kai amma ta ki yarda wanda ke nuna ta ji kunya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@_adunn_ade0:

"Wo, wannan daliba za ta sha hukunci."

@Ifeoluwa8557 ta ce:

"Ji karshen jin kunya."

@lovemelody717:

"NYSC ya yiwa Arike haka."

@vickidin:

"NYSC zai sauke maka kankanba."

A gefe daya, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wata matashiyar budurwa a manhajar TikTok.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya: Mata tazo neman magani wajen boka, ya dirka mata ciki a Kano

Budurwar dai ta nuna mummunan illa da aika-aikar da wata yar aiki da mahaifiyarsu ta kawo daga kauye ta yi mata inda ta kona mata fuska.

Kamar yadda kyakkyawar matashiyar ta bayyana, ta ce yar aikin da kanta ta fallasa abun da ta aikata inda ta ce ta zuba mata wani sinadari ne a cikin man shafarta wanda ya kai ga kona mata fuska.

Asali: Legit.ng

Online view pixel