Shugaban INEC Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Jam’iyyun Siyasa 18 a Abuja

Shugaban INEC Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Jam’iyyun Siyasa 18 a Abuja

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta zauna da jam'iyyun siyasan Najeriya don tattaunawa wasu batutuwan da suka shafi zabe
  • An bayyana adadin mutanen da ke da katin zabe a Najeriya yayin da zaben ya saura wata daya da 'yan kwanaki kadan
  • Jam'iyyun siyasa 18 a Najeriya na ci gaba da shiri don tabbatar da nasu ne ya hau kujerar mulki a bangarori daban-daban na Najeriya

FCT, Abuja - Yanzu muke samun labarin cewa, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu ya shiga wata ganawa da shugabannin jam'iyyun siyasa 18 a hedkwatar hukumar da ke Abuja, rahoton Vanguard.

Ganawar ta farko a wannan shekarar an tsara ta ne don mika adadin wadanda za su kada kuri'u a zaben 2023 da ke kamar yadda sabon kundin zabe na 2022 ya tanada.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Hukumar Zabe ta INEC ta Bayyana Yawan 'Yan Najeriya da Zasu Kada Kuri'a a Zaben 2023

Cikin wadanda suka halarta akwai shugabannin jam'iyyun APC, PDP, Labour da NNPP da dai sauransu.

INEC ta fadi adadin masu kada kuri'a a zaben 2023
Shugaban INEC Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Jam’iyyun Siyasa 18 a Abuja | Hoto: dailypost.com
Asali: UGC

An fadi adadin wadanda suka cancanta su kada kur'a a zaben 2023

A yayin ganawar, Mahmud Yakubu ya shaidawa jam'iyyun cewa, akalla mutum 93,469,008 ne suka yi rajistar yin zabe a Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, jihar legas kadai na da adadin masu kada kuri'u 7,060,195, sai kuma jihar Kano 5,921,370 da Kaduna mai jama'a 4,335,208.

Batu na jinsin da za su kada kuri'u, an ce maza 49,054,162 ne adadin masu kada kuri'un sai kuma mata 44,414,846, rahoton TheCable.

A bangaren shekaru kuwa, matasa masu shekaru 18 zuwa 34 sun kai akalla 37,060,399, wato kaso 39.66% na jumillar masu kada kuri'u.

A bangaren sana'a kuma, dalibai sun kai 26,027,481 a adadin masu akda kuri'a a Najeriya.

Akwai yiwuwar a dage zabe, inji INEC

Kara karanta wannan

Kwararan Dalilai 5 Dake Nuna Cewa Wajibi CBN Ya Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira

A wani labarin kuma, kun ji yadda hukumar zaben ta bayyana yiwuwar a dage zaben 2023 ko kuma a soke yinsa.

Wannan na zuwa ne duba da yadda tsaron kasar ke kara tabarbarewa, ga kuma babban zaben shugaban kasa na tafe cikin kankanin lokaci.

'Yan Najeroya na ci gaba da nuna damuwa kan tabbacin yin zabe, gwamnatin Buhari ta ba da tabbaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.