N1,090 Na Kashe a Rajistar Shiga Jami’a, Dan Najeriya Ya Tuna Rayuwar Baya

N1,090 Na Kashe a Rajistar Shiga Jami’a, Dan Najeriya Ya Tuna Rayuwar Baya

Wani dan Najeriya mai suna Sir Jarus ya yada wani rubutu a Twitter, ya bayyana yadda karatu ke da sauki a shekarun baya

  • A cewarsa, ya tuna yadda ya biya N40 a matsayin kudin makaranta JSS1 a 1994 kana ya kashe N1,090 a matsayin kudin rajistar shiga jami'a, har da wurin kwana a 2001
  • Ya ce, dukkan kudin da ya kashe daga Firamare zuwa kammala digiri bai kai N200k ba, kudin shiga wata jami'ar a yanzu

Wani dan Najeriya mai suna Sir Jarus ya yada adadin kudaden da ya kashe na yin karatun boko a rayuwarsa; daga firmare zuwa jami'a.

A cewarsa, ya taba biyan kudin rajistar shiga karamar sakandare JSS1 N40 a shekarar 1994.

Hakazalika, ya ce lokacin da ya kammala sakandare, ya shiga jami'a a 20221, kuma kudin da ya kashe na rajista da kudin wurin kwana a shekarar gaba daya N1,090 ne.

Kara karanta wannan

Ban Kashe ya Kai N200K ba Tun Daga Firamare har Jami'a: 'Dan Najeriya ya Bayyana Rasit din Kudin Makarantarsa

Ya kara da cewa, a ajin karshe a jami'ar da ya yi ta Obafemi Awolowo, N15,000 kadai ya kashe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya fadi nawa ya kashe a ilimin boko, mutane sun girgiza
N1000 na kashe a rajistar shiga jami'a, dan Najeriya ya tuna rayuwar baya | Hoto: @sirjarus/TikTok
Asali: UGC

Ya kara da cewa, dukkan kudin da ya kashe tsakanin Firamare da Jami'a bai kai N200,000 ba idan za a hada.

Ya rubuta:

"Zangona na farko a JSS1 kudin makaranta N40 (Naira arba'in ne) a shekarar 1994. Na biya N1,090 (Naira duba daya da Naira casa'in) a matsayin kudin rajistar shiga jami'a aji daya da wurin kwana a shekarar 2001.
"Na biya 15k ko makamancin haka a ajin karshe. Dukkan kudin da aka kashe a karatuna daga firamare zuwa jami'a kasa da <N200k ne."

Martanin jama'a a kafar sada zumunta

@sharperleinado:

"Najeriya ta kasance kuma har yanzu tana nan a matsayin mai kyau da yawanmu. Mun dai mora ta wasu hanyoyin."

Kara karanta wannan

An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023

@VOluwayemi:

"Na yi imanin cewa duk da kasancewar arahar karatunka ba ya nufin iyayenka sun ji saukin biyan kudin a wannan lokacin. Karatu na a jami'ar Ife bai kai 50k har na gama. Karatu kyauta ne, a makarantun gwamnati, ga firamare da sakandare."

@KalimatSuleman:

"A yanzu kuma suna son dauke wannan romo ga daliban Najeriya tare da kakaba kusu laifin hankali, kamar rancin dalibai bayan kara kudin makarantan ta yadda wasu ba za su iya biya tare da zaftare daukar nauyin karatun gaba sakadare."

@yemileel:

"Akwai matukar sauki yallabai."

@segun_are:

"Ilimi ba damfara bace, Na zuba jarin 200k amma ina kwasan daruruwan ninkin haka."

A yanzu dai a Najeriya babu abin da ya fi daukar hankali kamar batun kudin makaranta, jami'o'in kasar sun kara kudi mai yawa kan dalibai.

Akwai lokacin da Kwankwaso ya nemi dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar da ya rage kudin makaranta a jami'arsa da ke Yola.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Wani matashi ya yi tsaurin ido, ya sace mahaifinsa, an ba kudin fansa N2.5m

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.